An Kashe Mutum Akalla 70 A Yaki Tsakanin HKS Da Yan Tawaye A Kudancin Kasar Siriya
Published: 7th, March 2025 GMT
An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar.
Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a.
SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a.
Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a cikin watan Desemban da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa an kashe sojojin HTS akalla 16 a fafatawar jiya Alhamis, a bakin tekun Medeteranian a cikin lardin Lantakiya, inda Alawiyawa da musulmi mabiya mazhabar shia suka fi yawa a kasar.
A wannan yankin ne sansanin sojojin kasar Rasha suke ayyukansu a bakin ruwan Medeteranian. Alawiyawa sun aikwa sakonni a shafin Facebook inda suke bayyana cewa ta yaya, gwamnatin HTS zata yi amfani da hare-haren jiragen yakin helkomta a kansu bayan sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman hakkinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Siriya Ya Bukaci MDD Ta Dagewa Kasarsa Takunkuman Tattalin Arziki
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude.
Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace.
Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki. Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD sun dorawa gwamnatin tsohon shugaban kasar Bashar al-asada takunkuman tattalin arziki, don bawa yan tawayen da suke taimakawa nasara a yakin basabsan da aka dauki shekaru kimani 14 ana fafatawa a kasar.
Ya zuwa yanzun dai kasashen Burtaniya da tarayyar Turai da kuma Amurka duk sun daukewa kasar wasu takunkuman tattalin arzikin. Amma har yanzun akwai wasu da dama wadanda ba’a dauke ba.