Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Published: 7th, March 2025 GMT
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania.
Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II.
A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta Nato ba.
Shugaban yace EU zata gaggauta tattarawa harkokin tsaron kasashen EU saboda bunkatashi da sauri.
De Leyen ya kara da cewa ba zai yu a tattauna dangane da yakin a Ukraine ba tare da ita kasar Ukraine ko kasashen turai ba. Kasashen kungiyar 26 daga cikin 27 sun amince da wannan matin da suka fara dauka in banda kasar Hungary.
Volodomir Zelesky na kasar Ukraine ya isa taron kafin a fara shi a birnin Brssels, ya kuma godewa kasashen na Turai kan wannan kokarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Gabatar Da Tayin Shiga Tsakanin Don Sasanta Indiya Da Pakisatan
A dai-dai lokacinda kasashen Indiya da Pakisatn suke tada jijiyoyin wuta kan wani harin ta’addanci da ya kai ga mutuwar mutane 27 masu yawon shakatawa a yankin Kashmir na kasar Indiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gabatar da tayin shiga tsakani don dai-daita tsakanin kasashen biy.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka, a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa Iran tana da dangantaka mai karfi tsakaninta da kasashen biyu, kuma makobta ne kuma yan uwa wadanda suke da tsohuwar dangantaka ta al-adu a tsakaninsu na karnuka, ba za muyi kasa a guiwa wajen sasantasu ba, idan sun bamu wannan damar.
A cikin makon da ya gabata ne wasu yan bindiga suka bude wuta kan wasu maso yawan shakatawa a yankin Kashmir na kasar Iran inda mutane 27 suka mutu. Gwamnatin Undiya tana zargin Pakistan da hannu dumu-dumu a cikinsa, a yayinda gwamnatin kasar Pakisatan ta musanta hakan ta kuma yi allawadai da harin. Amma ta kara da cewa idan indiya ta kuskura ta yi amfani da makami a kanta to zata rana.
A daren jamm’an da ta gabata dai bangarorin biyu sun kai ga musayar wuta a tsakaninsu a kan iyakokin kasashen biyu.
Ministan ya bayyana cewa kasar zata yi amfani da ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Islamabad da kuma New Delhi don shiga tsakanin su idan sun amince da hakan.
Kasashen indiya da Pakistan dai sun dade suna takaddama kan mallakar Yankin Kashmir kuma sun sha shiga yaki saboda hakan.