Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi
Published: 7th, March 2025 GMT
Bayan da Amurka ta sanar da sanya karin haraji, kasashen Canada da Mexico da ma Sin dukkan sun dauki matakan ramuwar gayya. A ranar 4 ga wata, bi da bi ne ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ma kwamitin kula da dokokin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar sun sanar da jerin matakai na tinkarar matakan haraji na Amurka.
A hakika, al’ummar kasar Amurka suna sane da me matakan haraji da Trump ya dauka za su haifar musu. Kamar yadda wani dan kasar ya ce, “idan an samu hauhawar farashi na kaso 25%, mu kanmu ne za mu biya kudin, a maimakon gwamnati ko mutanen kasar Mexico.” Abin hakan yake, duk da cewa matakin haraji ya lalata dokokin cinikin kasa da kasa tare da haifar da rashin tabbas ga farfadowar tattalin arzikin duniya, amma daga karshe, kamfanonin kasar Amurka da ma al’ummar kasar ne za su dandana kudarsa. Daidai kamar yadda Ben Ayers, masanin ilmin tattalin arziki na kasar Amurka ya ce, “Karin iyalai a Amurka za su kara kimtsa wa shiga yanayin tattalin arziki mara tabbas da za su fuskanta a shekarar 2025.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi Ya Ce Kasar Sin Za Ta Magance Cin Zarafin Da Amurka Ke Yi Ita Kadai
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin.
Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida.
Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci, da nuna adawa da kariyar cinikayya, da kare daidaito da adalci a duniya.
Yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Uzbekistan Bakhtiyor Saidov, duk dai a wannan ranar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashe masu ra’ayi iri daya, wajen kiyaye damawa da kowa da kowa, da kare daidaito da adalci, da kuma nuna adawa da kariyar cinikayya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp