An yi garkuwa da ɗan uwan Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
Published: 7th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su.
Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa akwai ƙaninsa Ishaya Kukah na cikin waɗanda aka kama.
“Yayana Ishaya, shi kaɗai ne namiji a cikin waɗanda aka sace; sauran mata da yara ne, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare,” in ji shi.
Kukah ya ƙara da cewa har ya zuwa lokacin da yake zantawa da wakilinmu, babu wata tuntuɓa da masu garkuwar suka yi dangane da neman kuɗin fansa.
“Muna yi musu addu’ar Allah ya kare su yayin da muke jiran kowane kira,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an dawo da waɗanda lamarin ya rutsa da su lafiya, yana mai jaddada cewa galibin waɗanda aka sace mutane ne masu rauni.
Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi wa wakilinmu ƙarin bayani kan lamarin, amma har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ba.
Mazauna yankin na ci gaba da yin kira da a tsaurara matakan tsaro domin daƙile matsalar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kanwan Katsina Ya Yabi Gwamnatin Katsina Kan Farfado Da Al’adar Hawan Durbar
Hakimin Ketare kuma Kanwan Katsina, Alhaji Usman Bello Kankara, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa karɓar jakadun ƙasashe goma daga sassa daban-daban na duniya a lokacin bukukuwan Sallah na bana.
A cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwar diflomasiyya ba wai kawai zai bai wa duniya damar ganin al’adun gargajiya masu ɗimbin tarihi na jihar ba, har ila yau zai buɗe ƙofofin zuba jari da haɗin gwiwar ƙasashen waje.
Alhaji Usman Bello Kankara ya kuma jinjinawa gwamnati bisa jajircewarta wajen farfado da tsohuwar al’adar Sallah Durbar da ke da tarihin fiye da shekaru ɗari a Jihar Katsina.
“Gwamnatin Jihar Katsina ta cancanci yabo bisa irin ƙoƙarinta na farfado da tsohuwar al’adar Sallah Durbar da ke da dogon tarihi a jihar.” In ji shi.
A cewarsa, gyaran kujerun masu kallo a fadar sarkin Katsina da ta Daura, da kuma tsohon gidan gwamnati, ya taimaka sosai wajen ƙara jin daɗin baƙi da suka halarci jerin gwanon Sallah.
Kanwan Katsina na daga cikin Hakimai da masu rike da sarautun gargajiya da suka raka Mai Martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman, wajen gudanar da bukukuwan Sallah Durbar na bana a birnin Katsina.
Ranar farko ta jerin gwanon Durbar ta gudana ne a ranar Sallah, inda Musulmi daga sassa daban-daban na jihar suka halarta tare da iyalansu da dangi.
Ranar ta biyu ta kasance ranar kai gaisuwar Sallah zuwa gidan gwamnati, wanda Sarkin Katsina ya jagoranta tare da rakiyar hakimai da masu sarauta, inda suka kai gaisuwa ga Gwamna Malam Dikko Umar Radda a tsohon gidan gwamnati na Katsina.
An gudanar da jerin gwanon Durbar cikin kyan gani, inda aka ga sarakuna da fadawansu cikin kayan gargajiya, da dawakan da aka kawata cikin kyau, tare da dimbin jama’a da suka shaida bukukuwan.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarta har da Jakadan ƙasar Bulgaria a Najeriya, Yanko Yordanov, da wasu jakadu tara daga ƙasashe daban-daban tare da iyalansu, waɗanda Gwamnatin Jihar Katsina ta karɓa domin halartar wannan biki mai tarihi.
Wakilan Kanwan Katsina a wannan jerin gwanon sun haɗa da dukkanin dagatai a gundumar Ketare, mambobin majalisar gundumar Ketare da kuma dangin Kanwan Katsina.
Shekarar bana ta nuna zagayowar karo na 25 da Kanwan Katsina ke halartar bukukuwan Sallah Durbar tun bayan naɗinsa da aka yi a shekarar 2000 daga marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Muhammadu Kabir Usman.
Release/Adamu Yusuf