HausaTv:
2025-04-06@21:39:55 GMT

 Nigeria: Hukumar EFCC Ta  Yi Wa Tsouwar Ministar Harkokin Mata Tambayoyi

Published: 7th, March 2025 GMT

Hukumar da take yaki da yi wa tattalin arzikin kasar  Najeriya zagon kasa, ta yi wa tsohuwar ministar harkokin mata Uju Kennedy,tambayoyi masu alaka da zargin da ake yi mata akan aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da wasu kudade da sun kai Naira miliyan 138.4 a karkashin kasafin kudin ma’aikatar tata a 2023.

Da safiyar jiya Alhamis da misali 11: na safe ne tsohuwar ministar ta isa babbar shalkwarar hukumar ta EFCC dake birnin Abuja,inda ta amsa tambayoyin da aka yi mata.

Majiyar hukumar ta EFCC ta ce da akwai wasu kudade da aka bai wa ma’aikatar a karkashin shirin nan na p-Bat cares, amma sai aka karkata su zuwa asusun tsohuwar ministar.

Uju tana cikin minsitocin da  shugaban kasa Bola Tinubu ya sallama daga aiki a cikin watan Oktoba na 2024.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

WTO / IMF : harajin Trump, zai nakasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya

Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da asusun lamuni na duniya (IMF) sun nuna damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki daga sabbin harajin da gwamnatin Trump ta laftawa duniya, suna masu gargadin cewa hakan zai iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, WTO ta yi hasashen cewa harajin Amurka da ya hada da wanda aka gabatar a farkon wannan shekara zai iya rage cinikin hajoji a duniya da kashi 1 cikin 100 a shekarar 2025, wanda zai kaucewa hasashen da ta yi a baya na fadada cinikayya.

Rahoton ciniki na duniya na WTO, wanda aka fitar a watan Oktoban bara, ya yi hasashen cinikin kayayyaki a duniya zai karu da kashi 3 cikin 100 a bana, saidai karuwar rikicin siyasa da rashin tabbas kan manufofin tattalin arziki a yanzu sun sanya shakku sosai kan wannan hasashen.

Darakta-Janar na WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa matakan harajin na iya rikidewa zuwa yakin cinikayya, wanda zai kai ga daukar matakin ramuwar gayya daga wasu kasashe da kuma kara cutar da kasuwancin duniya.

Ita ma a nata bangaren, shugabar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta bayyana irin wannan damuwar a ranar Alhamis, inda ta bayyana irin hadarin da harajin na Amurka ke haifarwa ga daidaiton tattalin arzikin duniya.

Yayin da IMF ke ci gaba da tantance tasirin lamarin, ta yi gargadin cewa wadannan matakan za su iya dagula hasashen ci gaban da aka samu a duniya da kuma haifar da rashin tabbas.

Sabon harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a baya-bayan nan, wanda zai fara aiki a ranar Asabar, ya sanya kashi 10% kan duk wasu kayayyakin da ake shigowa da su kasar waje, tare da karin haraji kan kasashen da ke da gibin kasuwanci mafi girma da kasarsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun soke gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah
  • Araqchi: Iran ba ta da matsala game da tattaunawa amma ba za ta lamunci yi mata barazana ba
  • An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36
  • ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
  • Minista Ya Nemi A Mayar Da  NYSC Shekaru 2
  • WTO / IMF : harajin Trump, zai nakasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya
  •  Falasdinawa 86 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata
  • Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata
  • Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike
  • Iran Ta Yi Allawadai Da Kudurin Da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD Ta Amince A Kanta