Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
Published: 7th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da matakan da suka wajaba na cimma nasarar tsare-tsare masu inganci, na bunkasa rundunar sojin kasar Sin na shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojin kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne a Juma’ar nan, yayin da yake halartar taron rukuni na tawagar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin PLA, da rundunar ‘yan sandan kasar, a wani bangare na taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Bayan Shekaru 10 Madrid Da Barcelona Zasu Sake Yaɗuwa A Wasan Ƙarshe Na Copa Del Rey
Manyan kungiyoyin kwallon kafa Barcelona da Real Madrid zasu sake haduwa a wasan da ake yima kallon wasa mafi kayatarwa da akeyi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a halin yanzu.
Manyan kungiyoyin biyu duka na da dadadden tarihin iya taka leda da nuna kwarewa a harkar kwallon kafa, nasarorin da suka samu a kwallo ya sa ana yimasu kallon gagarabadau kokuma ace daukakakkun kungiyoyin kwallon kafa a Duniya.
UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago Copa Del Rey: Real Madrid Ta Buƙaci A Sauya Alƙalin Wasa A Karawarta Da BarcelonaYau Asabar Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe na kofin Copa Del Rey a filin wasa na De La Cartuja dake birnin Sevilla, Barcelona ta doke Athletico Madrid da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga kafin ta kawo wannan matsayi.
Hakazalika Real Madrid ta fitar da Real Sociedad a wasan na kusa da na karshe da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga tsakaninsu, alkalin wasa Ricardo De Burgos Bengoatxea ne zai jagoranci wasan duk da rashin yarda da Real Madrid ta nuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp