Aminiya:
2025-04-13@07:25:04 GMT

Zan sasanta Akpabio da Natasha — Ministar Harkokin Mata

Published: 7th, March 2025 GMT

Ministar Harkokin Mata, Imaan Suleiman Ibrahim, ta yi alƙawarin sasanta Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida bayan kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a ya same ta da laifin karya dokokin majalisar.

Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC

Yayin da ta ke magana da manema labarai bayan taron bikin Ranar Mata ta Duniya, ministar ta bayyana takaicinta kan dakatarwar da aka yi wa Natasha.

Ta ce, “Abin takaici ne kuma bai kamata ya faru ba. A majalisa ta baya, muna da mata Sanatoci guda tara, amma yanzu huɗu ne kawai suka rage.

“Ba ma son rasa kowace mace a majalisa, sai dai mu ƙara yawansu.”

Ta kuma tabbatar da cewa ana ƙoƙarin shawo kan lamarin.

“Za mu tabbatar da cewar an samu zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar da cewa an yi adalci.

“Shugaban Majalisar Dattawa da kansa ya ce a shirye suke domin a sasanta. Za mu zama masu shiga tsakani don haɗa kan ɓangarorin biyu da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin maza da mata a shugabanci,” in ji ta.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan yadda mutane daban-daban ke tofa albarkacin bakinsu kan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin Natasha da Akpabio.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: cin zarafi dakatarwa Ministar Harakokin Mata zargi

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya

Kungiyar Afica city of Refugee ta gabatar da taron bukatar da kuma muhimmancin samun zaman lafiya a tsakanin Makiyaya da Manoma a garin Saka wanda ya ke karkashin jagorancin gundumar ci gaba ta Karshi da Uke,Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa saboda a tattaunakan lamarin daya shafi zaman lafiya tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma.

Mutane da dama ne suka samu halartar taron wanda aka yi a Saka a makarantar Sakandare ta Saka daga cikin Shugaban kungiyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista na Karamar HUkumar Karu Reberend Timothy.

Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital

Reberend Justin darekta wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar ya yi jawabi ne mai daukar hankali kan muhimmancin zaman lafiya,shi ma Sarkin Saka,Injiniya Adamu ya nuna farincikinsa dangane da shi taron.

A na shi jawabin Bound Bradam ya yi kira da makiyaya Fulani da manoma da cewar su hada kansu da Sarakuna,Hakimai,Dagatai,da masu Unguwanni, domin habaka,da kuma inganta harkar zaman lafiya a tsakaninsu,a kuma kara da cewa yana son Fulani makiyaya a zuciyarsa, hakan ya sa yake ta ta duk yin abinda zai iya ba domin komai bas a don ya ga an ci gaba da zaman lafiya tsakanin su Manoma da Fulani makiyaya wadanda a shekarun da suka gabata ba jin tsakaninsu,zama ne suke na ‘yan’uwantaka da zumunci domin kuwa suna amfana da juna.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amnesty Ta Zargi  Rundunar “RSF” Ta Sudan Da Cin Zarafin Mata
  • Sharhi: Tattaunawa Zagaye Na Farko Tsakanin Iran Da Amurka A Oman
  • Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
  • Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba —Ganduje
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  • Iyaye Mata Sun Bukaci A Rika Samar Da Kayayyakin Bada Tazarar Haihuwa Akan Lokaci
  • Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
  • An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
  • Babu Wani Saɓani Tsakanin Tinubu Da Shettima — Jigon APC
  • Majalisar Kano Ta Yi Murna Da Lambar Yabo Da Jaridar LEADERSHIP Ta Bai Wa Abba