Yahudawa 800 Sun Kutsa Cikin Kasar Lebanon A Yau Juma’a
Published: 7th, March 2025 GMT
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya.
Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot.
A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka.
Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya Alhamis dai rundunar sojan kasar ta Lebanon ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa; Duk da cewa a akwai tsagaita wutar yaki amma Isra’ila tana ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon ta kasa, ruwa da kuma sama.” Sanarwar ta kuma ce; Abinda Isra’ilan take yi,barazana ce ga zaman lafiya a cikin Lebanon da kuma wannan yankin.
Haka nan kuma rundunar sojan kasar ta Lebanon ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya suna ci gaba da kai wa mutane hare-hare a garuruwan kudancin Lebanon da kuma yankin Bik’a.
A cikin wannan halin, mutanen kudancin kasar ta Lebanon suna ci gaba da komawa garuruwansu duk da cewa suna fuskantar hastarin kai musu daga sojojin mamaya.
Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba ne dai aka tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI bisa cewa za ta janye daga wuraren da ta yi kutse a cikin kwanaki 60, sai dai kuma hakan ba ta faru ba. Kungiyar Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi amfani da hanyoyin diplomasiyya domin tilastawa ‘yan mamayar janyewa, kafin a shiga wata magana ta daban.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata
A jiya Alhamis 3 ga wata ne, cibiyar daukar matakan gaggawa kan matsalolin kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa ta kasar Sin, gami da ofishin gwajin ayyukan fasahohin magance kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa na kasar, suka bullo da wani rahoto, kan binciken hare-haren yanar gizo da wasu kasashen waje suka kai kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9 da aka yi a birnin Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin a shekara ta 2025, gami da wasu muhimman ababen sadarwa dake lardin na Heilongjiang, inda ya shaida yadda kasar Amurka ta kaddamar da hare-haren intanet, kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 da aka yi a birnin Harbin, gami da wasu muhimman ababen sadarwa na lardin Heilongjiang, kana ana kyautata zaton cewa hare-haren sun samu goyon-baya daga gwamnatin Amurka. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a jiya Alhamis cewa, rahoton ya sake nanata cewa, Sin babbar kasa ce a duniya dake jin radadin harin intanet a jikinta, inda ta bukaci Amurka da ta kara waiwayar abubuwan da ta yi, da dakatar da shafa wa sauran kasashe bakin fenti. Kazalika, kasar Sin za ta ci gaba da daukar duk wani matakin da ya wajaba don kiyaye tsaron intanet a gida.
Har wa yau, yayin ziyararsa yankin Caribbean kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Antonio Rubio ya ce wai hanyar mota da kasar Sin ta shimfida a kasar Guyana ba ta da inganci sam, inda Amurka ta yi fatan samar mata da zabi na daban. Game da wannan batu, Guo Jiakun ya ce, ba kamfanin kasar Sin ne ya shimfida waccan hanyar mota ba, kuma tuni Guyana ta karyata labarin. Kasar Sin na ganin cewa, maimakon shafa wa kasar Sin bakin fenti, da rura wutar rikici, gara Amurka ta aikata wa sauran kasashe alheri na zahiri. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp