A wani bincike mai kayatarwa da wani rukuni na masana kimiyya na kasar Sin ya gudanar, ya gano wasu tsare-tsaren gudanar da rayuwa, a muhallin halittu mafi zurfi cikin kwarin teku da ake cewa “Mariana Trench”. Wurin da ake ganin shi ne mafi zurfi a sassan tekunan duniyar nan.

Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar “journal Cell”, cikin wasu takardun bincike 3, ya bayyana cewa, ta amfani da na’urar nutso a karkashin teku mallakin kasar Sin mai suna Fendouzhe, masu nazarin kimiyyar sun gano tsare-tsaren gudanar rayuwa na musamman, da ma albarkatun dake tattare da kananan halittu dake rayuwa a wurin mai tsananin zurfi, da halittu dangin kaguwa, da dangin kifaye dake wurin.

Kazalika, sakamakon binciken ya baiwa bil adama damar kara fahimtar yanayin rayuwar halittu a muhallin karkashin teku da zurfinsa ya kai mita 10,000, yayin da nau’o’in kwayoyin halittu, da yanayinsu, da tasirin rayuwarsu, ka iya baiwa masu bincike damar gudanar da nazari bisa sabbin kirkire-kirkire, ta yadda za a kai ga magance tarin kalubale masu nasaba da albarkatun halittu masu rai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar.

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata

Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin sunayen ’yan takara za su gudana daga ranar 25 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, 2025.

Shugaban ya ce, za a maido da jerin sunayen ’yan takarar da aka tura musu daga ranar 3 zuwa 10 ga Afrilu yayin da za a wallafa bayanan ’yan takarar daga ranar 11 zuwa 18 ga Afrilu, 2025.

Ya ƙara da cewa an shirya tattara fom ɗin tsayawa takara a ranar 19 zuwa 26 ga Afrilu yayin da jam’iyyun siyasa za su gabatar da fom ɗin takara daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 3 ga Mayu, 2025.

Ya ce, za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen daga ranar 27 ga watan Mayu har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2025.

Imam ya tabbatar wa jam’iyyun siyasa matakin da za a yi na gudanar da zaɓuka cikin ’yanci, gaskiya da adalci bisa wasu dokoki da jagororin gudanar da zaɓukan kansiloli.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Da CGTN Ta Gudanar Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Diflomasiyyar Sin
  • Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai
  • Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
  • An Bude Cibiyoyin Ciyar Da Masu Azumi A Dan Modi Na Garin Kafin Hausa
  • Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
  • ’Yan bindiga: Har yanzu Janar Tsiga na tsare bayan kwanaki 29
  • Yadda Ake Ayyukan Gina Ababen More Rayuwa A Jihar Zamfara 
  • Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni