Zuwa Karshen Fabarairu Yawan Musayar Kudaden Da Aka Adana Na Sin Ya Kai Dala Tiriliyan 3.2272
Published: 8th, March 2025 GMT
Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, zuwa karshen watan Fabarairun shekarar nan ta 2025, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin, ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2272, adadin da ya karu da dalar Amurka biliyan 18.2, sama da na karshen watan Janairu, wato karuwar kaso 0.
Wani jami’i mai aiki a hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai inganci, da fa’ida mai yawa, da juriya mai karfi, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: musayar kudaden
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kasar Aljeriya Ta Dakatar Da Zirga-Zirgan Jiragen Saman Kasar Zuwa Kasar Mali
Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar.
Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi.
Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger, Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar.
Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba.
Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen sama tsakanin kasashen biyu zai shafi al’amuran kasuwanci soai a kasashen yankin.