HausaTv:
2025-04-08@12:29:00 GMT

OIC Ta Yi Maraba Da Shirin Gwamnatocin Larabawa Na Sake Gina Zirin Gaza

Published: 8th, March 2025 GMT

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, Hussein Ibrahim Taha, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga shirin Larabawa na sake gina zirin Gaza.

Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar, taron da ya gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya a wannan  Juma’a, inda suka tattauna halin da ake ciki dangane da ayyukan wuce gonad a iri na Isra’ila a Falastinu.

A cikin jawabinsa, Sakatare-Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin sake gina zirin Gaza, wanda taron kolin kasashen Larabawa ya amince da shi, tare da jaddada hakkin al’ummar Palasdinu na ci gaba da zama a cikin kasarsu.

Baya ga haka kuma ya yi gargadi dangane da hadarin da ke tattare da matakan da Isra’ila take shirin dauka na korar Falastinawa daga yankunansu a Gaza, da kuam ammaye wasu yankuna a gabar yammacin kogin Jordan, yana mai cewa kungiyar OIC ba za ta taba  amincewa da hakan ba.

Babban magatakardar ya jaddada cewa, ba za a iya raba ko kuma maye gurbin hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu wato (UNRWA) da kuma muhimmiyar rawar da take takawa wajen yi wa miliyoyin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa hidima ba, yayin da ya jaddada bukatar a rubanya tallafin siyasa da kudade ga wannan hukumar.

Babban magatakardar ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da janyewar sojojin mamaya gaba daya daga Gaza, da kuma isar da kayayyakin jin kai ga al’ummar yankin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i.

Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga?

NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta

Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Dole ne Amurka ta tabbatar da cewa da gaske take yi a game da tattaunawa
  • An sake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv
  • NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu
  • Kasar Sin Na Shirin Gaggauta Karfafa Karfinta A Bangaren Aikin Gona
  • Sharhin Bayan Labarai: Zanga-Zanga A Kasashen Larabawa Ta Goyon Bayan Falasdinaw A Gaza
  •  Kasashen Iran, Rasha Da China Za Su Yi Taro A Moscow Domin Tattauna Batutuwa Da Dama
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi?
  • Rasha za ta bude ofishin jakadanci a Nijar nan ba da jimawa ba
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  •  Kungiyar Malaman Musulunci Ta  Duniya Ta  Yi Fatawar Wajabcin Taimakawa Falasdinawa