Al-Houthi: Mun Baiwa Isra’ila Wa’adin Kwanaki 4 Da Ta Kawo Karshen Killace Gaza
Published: 8th, March 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.
A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba da killace yankin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi, lamari ne mai matukar hadari.
Al-Houthi ya zargi Isra’ila da kin yin aiki da alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a kan Gaza, musamman dangane da ayyukan jin kai, yana mai cewa Hamas ta cika dukkanin alkawullanta da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, ta hanyar kiyaye wannan yarjejeniyar.
Har ila yau Al-Houthi ya yi Allah wadai da zafafa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankunan yammacin gabar kogin Jordan da kuma al-Quds, yana mai bayyana irin rawar da Isra’ila ke takawa wajen kara kai hare-hare kan Falasdinawa a matsayin laifin yaki.
Baya ga haka kuma, Ya soki yadda Amurka ke goyon bayan mamayar Isra’ila ido rufe a karkashin Shugaba Donald Trump, yana mai cewa goyon bayan Washington ya karfafa gwiwar Isra’ila wajen ci gaba da muzgunawa Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ke
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Kananan Hukumomi 749 Sun Gaza Bayar Da Cikakkun Bayanan Asusunsu
A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye.
“Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu.
“Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.”
Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba.
Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas.
“Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don tabbatar da cewa sun sami kasosu kai tsaye. Wannan ya faru ne saboda abubuwa da yawa na bukatar a magance su,” in ji ta.
Idan za a iya tunawa dai, Babban Bankin Nijeriya ya fara bayyana shugabanni da masu sa hannun a asusun bankuna na kananan hukumomi 774 da ke kasar a wani mataki na fara cin gashin kan kananan hukumomi.
Daraktan kula da harkokin shari’a na Babban Bankin Nijeriya, Kofo Salam-Alada, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin tabbatar da bin diddigin kudade.
“Wannan duk na cikin tsari sanin abokin hulda. Duk wanda zai zama mai sa hannu a asusun dole ne a bayyana shi.
“Tsarin yana ci gaba, kuma muna hadin gwiwa da ofishin akanta janar. Mun kuma rubuta wa kananan hukumomin,” inj i shi.
Sai dai kungiyar shugabnnin kananan hukumomin Nijeriya ta ce ba ta samu wata sanarwa daga babban bankin kasar ba dangane da bude asusun ajiyar banki.
Idan za a iya tunawa, a ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta tabbatar da ikon cin gashin kananan hukumomi 774 da ke kasar nan tare da haramta wa gwamnoni ci gaba da kula da kudaden da aka ware wa kananan hukumomi.
Kotun kolin ta kuma umurci Akanta Janar na Tarayya da ta biya kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsu, inda ta bayyana rashin fitar da kudaden da jihohi 36 suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Amma watanni takwas bayan yanke hukuncin, har yanzu ba a fara aiki da hukuncin cin gashin kan kananan hukumomi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp