Aminiya:
2025-03-09@12:15:23 GMT

Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano

Published: 8th, March 2025 GMT

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta rufe wani shagon da ake yin caca na zamani, wanda aka fi sani da “betting.

Mataimakin kwamandan hukumar a Kano, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano.

Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95  Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai

Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bisa dokokin Jihar Kano, kuma hukumar ta kai samame wajen kafin ta rufe shagon gaba ɗaya.

Aminudeen ya nuna damuwa kan yadda wasu Musulmai ke shiga harkar caca, musamman a lokacin azumin watan Ramadan.

A watannin baya hukumar ta haramta yin cacar “betting” lamarin da ya sanya ta fara farautar wuraren da ake yin cacar domin rufe su.

An fara aiki da dokokin shari’ar Musulunci a Kano tun shekarar 2000, kamar yadda ake yi a wasu jihohi 11 na Arewacin Najeriya.

Waɗannan dokoki sun haramta caca, karuwanci da shan giya a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ramadan Shari ar Musulunci

এছাড়াও পড়ুন:

Ramadan: Imani da Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa – Ministan Yada Labarai

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya.

Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya.

Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa.

“Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu.

“Duk da haka, a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke haduwa don yin addu’a, yin nazari, nuna jituwa da jinƙai ga juna, babu shakka, batutuwan imani da, siyasa da kuma mulki suna da dangantaka da jiya, yau da kuma gobe. Wajibi ne mu ci gaba da fahimtar yadda za mu tafiyar da su yadda ya dace.

“Sai dai, yayin da muke kokarin fahimtar alakar imani da siyasa da kuma mulki, muna kuma fuskantar kalubalen siyasa na ciki da waje, waɗanda ke tasiri ga yadda muke kallon hadin kan kasa a matsayin dunkulalliyar ƙasa,” in ji shi.

Ministan ya yaba da halartar manyan baki, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Cigaban Kiwo Dabobi, Malam Idi Mukhtar Maiha; da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Jakadan Najeriya, Ahmed Nuhu Bamalli. Haka nan, ya gode wa fitattun malamai, Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Ismaila Shehu, bisa gudummawar da suka bayar a wannan muhimmin tattaunawa.

Da yake yin tsokaci kan muhimmancin Ramadan, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan wata mai alfarma domin yin nazari da inganta hadin kai, da sabunta aniyar su ta bada gudunmawa ga ci gaban kasa.

Ya jaddada irin nasarorin da aka samu a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman sanya hannu kan kasafin kudi na Naira Tiriliyan 54, wanda ya ba da fifiko kan tsaro, ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.

Haka nan, Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa kan kirkirar Ma’aikatar Bunkasa Kiyo Dabobi ta Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya a kasa.

“Yayin da muke tafiyar da harkokin siyasa da mulki, tare da tasirin da suke da shi kan shawarwarin da muke yanke, yana da matukar muhimmanci mu zabi hanya madaidaiciya,” in ji shi.

A karshe, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi dabi’un soyayya, jinƙai, da jajircewa a lokacin Ramadan da bayan sa.

“Allahu ya albarkaci iyalanmu, ya shiryar da matakanmu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuranmu. Ramadan Kareem,” in ji shi.

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
  • Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda
  • Ramadan: Imani, Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa – Ministan Yada Labarai
  • Ramadan: Imani da Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa – Ministan Yada Labarai
  • ‘Yansanda A Legas Sun Kama Mutum 35 Da Ake Zargi Da Fashi Cikin Mako Guda
  • Hukumar Raya Arewa maso Yamma Ta Kai Ziyara Jihar Jigawa
  • Sojojin Isra’ila Sun Kai Hari A Kan Masallatan Nablus A Ranar Juma’ar Farko Ta Watan Ramadan
  •  Nigeria: Hukumar EFCC Ta  Yi Wa Tsouwar Ministar Harkokin Mata Tambayoyi
  • Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata