Bankin Duniya : Sake Gina Lebanon Yana Bukatar Dala Biliyan 11
Published: 8th, March 2025 GMT
Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar.
Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.
“Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya.
Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar.”
Sojojin Isra’ila sun fara kai farmaki kan sansanonin Hizbullah a kudancin Lebanon jim kadan bayan kaddamar da kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yiwa kawanya a watan Oktoban shekarar 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
A jiya Juma’a, an gudanar da taron dandalin tattaunawar kirkire-kirkire na kafofin watsa labaru na duniya karo na 4, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da gwamnatin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Qufu na lardin.
Taron dandalin mai taken “Musanya da yin koyi da juna da ma amfani da kimiyya da fasaha na kasancewa karfin wayewar kai a yayin da ake neman sauye-sauye da ci gaba”, ya samu halartar wakilai kusan 300 daga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin watsa labarai na kasashe da yankuna 95, da cibiyoyin masana na kasar Sin da na kasashen waje, da ma kamfanonin ketare da dai sauransu ta yanar gizo da kuma a zahiri. (Mai fassara Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp