Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla.

Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus.

Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin.

Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci gaba da cin zarafi da gwamnatin Isra’ila ke yi kan yankin yammacin kogin Jordan na daga cikin shirin gwamnatin kasar na mamaye yankin.

A watan Yulin 2024, Kotun Duniya (ICJ) ta yanke hukuncin mamayar da Isra’ila ta dade tana yi a yankunan Falasdinawa ba bisa ka’ida ba, inda ta bukaci a kwashe duk wasu haramtattun matsugunan da ke Yammacin Kogin Jordan da gabashin Quds.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila sun

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa.

Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama.

A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin  hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida.

Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu.

Bugu da ƙari, Ambaliyar ya haifar da cunkoson ababen hawa a birnin da ake fama da yawan zirga zirga.

Mazauna yankin da abin ya shafa sun shaidawa manema labarai cewa sun fusata bayan da gwamnati ta ƙi kawo musu agajin gaggawa.

 

rfi

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsawaita Rajistar Sabunta Shaidar Mallakar Fili: Gwamnatin Kano Ta Yi Barazanar Kwace Filaye
  • Jihar Kwara Za Ta Rufe Karbar Kudin Aikin Hajji A Ranar Juma’a
  • Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Dan jarida Ahmad Mansour ya yi shahada bayan sojojin Isra’ila sun kona shi da ransa a Gaza
  • Saudiyya ta bayar da wa’adin ficewar dukkanin masu aikin Umrah daga kasar
  • Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar
  • HOTUNA: Yadda zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta gudana a wasu biranen Nijeriya
  • Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo
  • Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
  • Gaza : adadin ‘yan jaridar da aka kashe ya haura 210