Ramadan: Imani, Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa – Ministan Yada Labarai
Published: 8th, March 2025 GMT
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya.
Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya.
Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa.
“Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu.
“Duk da haka, a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke haduwa don yin addu’a, yin nazari, nuna jituwa da jinƙai ga juna, babu shakka, batutuwan imani da, siyasa da kuma mulki suna da dangantaka da jiya, yau da kuma gobe. Wajibi ne mu ci gaba da fahimtar yadda za mu tafiyar da su yadda ya dace.
“Sai dai, yayin da muke kokarin fahimtar alakar imani da siyasa da kuma mulki, muna kuma fuskantar kalubalen siyasa na ciki da waje, waɗanda ke tasiri ga yadda muke kallon hadin kan kasa a matsayin dunkulalliyar ƙasa,” in ji shi.
Ministan ya yaba da halartar manyan baki, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Cigaban Kiwo Dabobi, Malam Idi Mukhtar Maiha; da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Jakadan Najeriya, Ahmed Nuhu Bamalli. Haka nan, ya gode wa fitattun malamai, Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Ismaila Shehu, bisa gudummawar da suka bayar a wannan muhimmin tattaunawa.
Da yake yin tsokaci kan muhimmancin Ramadan, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan wata mai alfarma domin yin nazari da inganta hadin kai, da sabunta aniyar su ta bada gudunmawa ga ci gaban kasa.
Ya jaddada irin nasarorin da aka samu a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman sanya hannu kan kasafin kudi na Naira Tiriliyan 54, wanda ya ba da fifiko kan tsaro, ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.
Haka nan, Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa kan kirkirar Ma’aikatar Bunkasa Kiyo Dabobi ta Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya a kasa.
“Yayin da muke tafiyar da harkokin siyasa da mulki, tare da tasirin da suke da shi kan shawarwarin da muke yanke, yana da matukar muhimmanci mu zabi hanya madaidaiciya,” in ji shi.
A karshe, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi dabi’un soyayya, jinƙai, da jajircewa a lokacin Ramadan da bayan sa.
“Allahu ya albarkaci iyalanmu, ya shiryar da matakanmu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuranmu. Ramadan Kareem,” in ji shi.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ramadan siyasa Yada Labarai Ministan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Ta Shirya Aiwatarda Yarjejeniyar Fahimta Tsakanin NTA, FRCN Da China Media Group
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Jakadan Sin a Najeriya, Mista Yu Dunhai, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa a yau alhamis. Ya ce, wadannan yarjejeniyoyi sun ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin watsa labarai da sadarwa, domin inganta dangantakar Najeriya da Sin.
Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun shafi musayar bayanai da fasahar zamani, wanda hakan zai inganta ƙwarewar gidajen watsa labaran Najeriya tare da ɗaukaka su zuwa matakin da ya dace da kyawawan ƙa’idojin duniya.
“Najeriya da Sin a matakin hulɗar diflomasiyya suna da ƙawance mai ƙarfi matuka. Wannan ya haifar da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta guda 10 a Beijing, kuma guda biyu daga cikinsu suna da nasaba da wannan ma’aikata. Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) ita ce cibiyar talabijin mafi girma a duk faɗin Afirka, tana da tashoshi sama da 100 da ke rufe dukkan yankuna tare da isa ga mutane sama da miliyan 200. Yana da matuƙar muhimmanci, kuma abin da NTA ke son cimmawa ta hanyar wannan haɗin gwiwa da Sin shi ne musayar labarai, fasaha, da bayanai wanda zai amfanar da ƙasashen biyu. Haka kuma, muna da irin wannan yarjejeniya da ɗaya daga cikin manyan gidajen rediyo a Afirka, wato Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN). Wadannan yarjejeniyoyi sun riga sun kammala, kuma Najeriya tana da niyyar cika nata ɓangaren,” in ji shi.
Ministan ya ce, bayar da sahihin bayani da labarai na gaskiya zai ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashe, don haka ya nemi haɗin gwiwa da Sin wajen yaƙi da labaran ƙarya, ɓata bayani da yada bayanai na bogi.
“Yada labaran ƙarya ƙalubale ne ga duniya baki ɗaya. Mun san cewa Sin tana ɗaukar wannan batu da muhimmanci sosai, haka kuma mu ma a Najeriya muna ɗaukar hakan da muhimmanci. Ba matsala ba ce da ke shafar Najeriya da Sin kaɗai; matsala ce ta duniya baki ɗaya, kuma muna son yin aiki tare da Sin don yaƙi da labaran ƙarya tare da inganta watsa labarai masu amfani da za su taimaka wajen bunƙasa al’umma,” in ji shi.
Idris ya bayyana wa Jakadan cewa, Najeriya na da ‘yancin watsa labarai a matsayin wani muhimmin bangare na manufofin gwamnatin Tinubu don ƙarfafa dimokuradiyya ta hanyar bayar da ingantattun bayanai.
“Kafafen watsa labarai a nan suna da ’yanci sosai. Tabbas, akwai wasu matsaloli a lokaci zuwa lokaci, wanda koyaushe muna aiki a kansu don ingantawa. Najeriya na da babbar ’yancin watsa labarai, kuma muna so mu ci gaba da hakan,” in ji shi.
Ministan ya kuma bukaci kamfanonin Sin su yi amfani da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin zuba jari a tattalin arzikin Najeriya.
A nasa jawabin, Jakada Dunhai ya ce a matsayinsa na sabon jakadan Sin a Najeriya, zai yi duk mai yiwuwa don ƙara ƙarfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ya nuna goyon bayansa ga shirin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Tinubu, wanda ke da nufin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa don samar da ci gaba mai dorewa.
“A matsayina na sabon jakada, ina ganin kaina a matsayin mai sa’a saboda na zo ne a lokacin da Najeriya ke karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, wanda ke da niyyar gina ƙasa mai ƙarfi. Haka nan, a karkashin jagorancin Shugaba Xi Jinping, Sin tana kan tafarkin sabunta ƙasa ta hanyar tsarin zamani na Sin,” in ji shi.
Jakadan ya tunatar da cewa a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a Beijing, Shugabannin kasashen biyu, Xi Jinping da Tinubu, sun amince da ɗaukaka dangantakar kasashen su zuwa babbar kawance ta fuskar diflomasiyya, wanda hakan zai buɗe sabon babi a dangantakar su.
Ya ce yana sa ran ganin yadda za a aiwatar da yarjejeniyoyin fahimta da aka kulla tsakanin NTA, FRCN da China Media Group, domin kafafen yada labarai suna da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen gina al’umma.
Jakadan ya bayyana jin daɗinsa cewa kafafen watsa labarai a Najeriya suna daidaito, gaskiya da adalci a labaran da suke watsawa, domin suna ƙoƙarin gabatar da cikakken bayani kan abubuwan da ke faruwa ga ‘yan Najeriya.
A bangaren zuba jari, Jakadan ya ce Shugaba Xi Jinping ya alkawarta dala biliyan 50 domin zuba jari a Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa, a matsayin ci gaba ga yarjejeniyoyin fahimta guda goma da aka rattaba hannu a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a baya-bayan nan.
Cov/Adamu Yusuf