FUD Ta Nada Abdullahi Yahaya Bello Daraktan Hulda da Jama’a
Published: 8th, March 2025 GMT
Shugaban Jami’ar TTarayyada ke Dutse a Jihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammed ya amince da nadin Malam Abdullahi Yahaya Bello, a matsayin Daraktan riko na Jami’ar daga ranar 1 ga watan Maris na 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardar jami’ar, Alhaji Abubakar Mijinyawa ya rabawa manema labarai a Dutse.
Sanarwar ta taya Malam Abdullahi murna tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi nasara wajen sauke nauyin da aka dora masa.
Malam Abdullahi Yahaya Bello shi ne ya kafa sashen yada labarai da hulda da jama’a na jami’ar a shekarar 2012 a matsayin jami’in hulda da jama’a na Jami’ar na farko.
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, ya ci gaba da zama mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na a shekarar 2023 kafin nadin da yake yi a yanzu a matsayin Mukaddashin Daraktan kula da hulda da jama’a na Jami’ar Tarayya ta Dutse.
“Ya halarci tarurrukan horaswa da bita kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a da dama, kuma memba ne a Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR), Memba a Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), hakazalika Memba, da sauran kungiyoyin ilimi da dama.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ramadan: Imani da Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa – Ministan Yada Labarai
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba ɗaya.
Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya.
Da yake jawabi kan taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,” Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa.
“Ina da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu.
“Duk da haka, a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke haduwa don yin addu’a, yin nazari, nuna jituwa da jinƙai ga juna, babu shakka, batutuwan imani da, siyasa da kuma mulki suna da dangantaka da jiya, yau da kuma gobe. Wajibi ne mu ci gaba da fahimtar yadda za mu tafiyar da su yadda ya dace.
“Sai dai, yayin da muke kokarin fahimtar alakar imani da siyasa da kuma mulki, muna kuma fuskantar kalubalen siyasa na ciki da waje, waɗanda ke tasiri ga yadda muke kallon hadin kan kasa a matsayin dunkulalliyar ƙasa,” in ji shi.
Ministan ya yaba da halartar manyan baki, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Cigaban Kiwo Dabobi, Malam Idi Mukhtar Maiha; da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Jakadan Najeriya, Ahmed Nuhu Bamalli. Haka nan, ya gode wa fitattun malamai, Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Ismaila Shehu, bisa gudummawar da suka bayar a wannan muhimmin tattaunawa.
Da yake yin tsokaci kan muhimmancin Ramadan, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan wata mai alfarma domin yin nazari da inganta hadin kai, da sabunta aniyar su ta bada gudunmawa ga ci gaban kasa.
Ya jaddada irin nasarorin da aka samu a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman sanya hannu kan kasafin kudi na Naira Tiriliyan 54, wanda ya ba da fifiko kan tsaro, ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.
Haka nan, Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa kan kirkirar Ma’aikatar Bunkasa Kiyo Dabobi ta Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya a kasa.
“Yayin da muke tafiyar da harkokin siyasa da mulki, tare da tasirin da suke da shi kan shawarwarin da muke yanke, yana da matukar muhimmanci mu zabi hanya madaidaiciya,” in ji shi.
A karshe, Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi dabi’un soyayya, jinƙai, da jajircewa a lokacin Ramadan da bayan sa.
“Allahu ya albarkaci iyalanmu, ya shiryar da matakanmu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuranmu. Ramadan Kareem,” in ji shi.
Rel/Adamu Yusuf