Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya.

Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na Maris, zai kuma kunshi karin kaso 100 bisa mai rapeseed, da tunkuza, da waken peas, yayin da kuma albarkatun teku, da naman alade da ake shigarwa Sin daga Canada, aka yi musu karin harajin kaso 25 bisa dari.

Mahukuntan kasar Sin sun ce matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da nuna banbanci a hada-hadar cinikayya, wanda ya tabbatar da cewa, matakan da kasar Canada ta dauka kan hajojin Sin da ake shigarwa kasar sun haifar da cikas, ga harkokin cinikayyar da aka saba gudanarwa tsakanin sassan biyu, kana sun illata halastacciyar moriyar kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

 Yahudawa 800 Sun Kutsa Cikin Kasar Lebanon A Yau Juma’a

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya.

Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot.

A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya Alhamis dai rundunar sojan kasar ta Lebanon ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa; Duk da cewa a akwai tsagaita wutar yaki amma Isra’ila tana ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon ta kasa, ruwa da kuma sama.” Sanarwar ta kuma ce; Abinda Isra’ilan take yi,barazana ce ga zaman lafiya a cikin Lebanon da kuma wannan yankin.

Haka nan kuma rundunar sojan kasar ta Lebanon ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya suna ci gaba da kai wa mutane hare-hare a garuruwan kudancin Lebanon da kuma  yankin Bik’a.

A cikin wannan halin, mutanen kudancin kasar ta Lebanon suna ci gaba da komawa garuruwansu duk da cewa suna fuskantar hastarin kai musu daga sojojin mamaya.

Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba ne dai aka tsagaita wutar yaki a tsakanin Lebanon da HKI bisa cewa za ta janye daga wuraren da ta yi kutse a cikin kwanaki 60, sai dai kuma hakan ba ta faru ba. Kungiyar Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi amfani da hanyoyin diplomasiyya domin tilastawa ‘yan mamayar janyewa, kafin a shiga wata magana ta daban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Senegal, Ta Karbi Wasu Sansanonin Sojin Faransa A Kasar
  • Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
  • Qatar Ta Ce Bata Goyon Bayan Yakin Don Warware Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Oficin Jakadan Iran A MDD Ya Ce Babu Wani Sako Da Suka Karba Daga Shugaban Kasar Amurka
  • Fararen hula 162 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan a lardunan gabar tekun Syria
  • Matakin Amurka Na Kakaba Haraji Kan Kayayyakin Sin Ta Fakewa Da Batun Sinadarin Fentanyl Bai Dace Ba
  •  Yahudawa 800 Sun Kutsa Cikin Kasar Lebanon A Yau Juma’a
  • An Kashe Mutum Akalla 70 A Yaki Tsakanin HKS Da Yan Tawaye A Kudancin Kasar Siriya
  • Yansanda A Najeriya Sun Kama Yan Kasar Pakistan Biyu Da Hakanni Wajen Sake Yan Kasashen Waje A Kasar