Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata
Published: 8th, March 2025 GMT
C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai.
5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa.
6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog zaya. Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Tsimin rake Kenan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abubuwan Sha
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi Ya Tafi Saudiyya Domin Halartar Taron OIC
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira.
A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za a gudanar da taron a yammacin ranar Juma’a, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta bukaci taron ne domin jawo hankalin kungiyar OIC, a matsayinta na babbar kungiya a duniyar musulmi, kan batun da ya shafi al’ummar musulmi da kasashen musulmi.
Shirin shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawan Gaza da kasarsu ta asali ya fuskanci tofin Allah tsine a duniya.
“Iran ne ta gabatar da bukatar taron domin martani wa shirin na Trump.