Aminiya:
2025-04-13@14:35:09 GMT

NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya

Published: 8th, March 2025 GMT

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, wadda shugabanta, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna.

Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol

NMDPRA ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man ne a jihohin Abia da Delta da kuma Edo.

“Za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a Jihar Edo.

“Za kuma a buɗe Matatar MB wadda za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum a Jihar Delta, sai Matatar HIS wadda ita kuma za ta riƙa tace ganga 10,000 a kullum a Jihar Abia.”

Hukumar ta ce sabbin matatun uku idan an kammala su gaba ɗaya za su iya tace ganga 140,000 na man fetur duk rana.

Bayanai daga hukumar ta NMDPRA sun nuna cewa Nijeriya na da matatun man fetur tara, ciki har da sabuwar matatar Dangote da ke birnin Legas.

Waɗannan matatu na tace ganga 974,500 a duk rana, yayin da Matatar Dangote kaɗai ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matatar Dangote NMDPRA

এছাড়াও পড়ুন:

Asusun Tallafawa Dalibai Da Rancen Kudi Ya Koka Akan Ayukkan Wasu Jami’o’in Nijeriya

Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.

 

Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba.

 

Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade su da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.

 

“Wannan matakin na hana mahimman bayanan kuɗi daga ɗalibai ba rashin da’a ba ne kawai amma cin zarafi ne kai tsaye ga ƙa’idodin da aka kafa NELFUND a kai. “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a kan duk wata cibiya da aka samu da aikata irin wadannan ayyukan yaudara.”

 

 

Ya shawarci dukkanin cibiyoyi da su tabbatar da gaskiya tare da yin aiki tare da Asusun don tabbatar da isar da ayyukan sa yadda ya kamata.

 

Mista Sawyerr ya jaddada cewa manufar NELFUND ita ce fadada hanyoyin samun ilimi mai zurfi ta hanyar sauke nauyin kudi a kan daliban Najeriya da iyalansu, daidai da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asusun yana tabbatar wa ɗalibai da jama’a jajircewar sa na yin riko da gaskiya, yin adalci, da samun nasarar aiwatar da shirin rancen ɗalibai a faɗin ƙasar.

 

HAKURI OLUMATI

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu
  • Saudiya Tace Shigo Da Agaji Cikin Gaza Bai Da Dangantaka Da Tsagaita Wuta
  • Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari
  • Asusun Tallafawa Dalibai Da Rancen Kudi Ya Koka Akan Ayukkan Wasu Jami’o’in Nijeriya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
  • Gwamnati ta gargaɗi jihohi 30 kan ambaliyar ruwa
  • Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji
  • E.U.  ta dauki wasu sabbin matakan kalubalantar harajin fito na Amurka