Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda
Published: 8th, March 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris.
NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar DattawaSP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47.
Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da wuƙaƙe da adduna da wayoyin hannu da wasu layu.
Ya bayar da sunayen matasan da ke hannu da suka haɗa da — Shukurana Salihu mai shekaru 25 da Rabi’u Dahiru mai shekaru 35 da Ya’u Idris mai shekaru 30 duk daga Jihar Katsina sai kuma Muktar Sani mai shekaru 30 daga yankin ’Yandodo na unguwar Hotoro da ke Kano.
SP Kiyawa ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan ababen zargin da ke tsare a sashen binciken miyagun laifuka na hedikwatarsu da ke Bompoi.
Rundunar ’yan sandan wadda ta ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike, ta kuma jaddada ƙudirinta na kawo ƙarshen duk wasu miyagu a faɗin jihar.
Ta kuma miƙa godiya ga al’umma dangane da goyon baya da haɗin kan da take samu a ƙoƙarinta na yaƙi da masu tayar da zaune tsaye.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Kano Jihar Katsina ababen zargin mai shekaru
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Gwamnan Oyo, Omololu Olunloyo, Ya Rasu Yana Da Shekaru 89
Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983.
Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp