HausaTv:
2025-04-08@12:44:26 GMT

A ranar Mata Ta Duniya, Hamas Ta Yi Allawadai Da Kashe Mata 12,000 A Gaza

Published: 8th, March 2025 GMT

A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu.

Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su.

Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina

A ƙauyen Maikuma, da ke cikin ƙaramar hukumar Dandume ta Jihar Katsina, ana zargin wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 4 sannan suka sace a ƙalla 45. Harin ya faru ne a daren Lahadi, lokacin da wata babbar tawagar ‘yan fashin ɗauke da makamai ta kai farmaki a cikin al’umma.

Shaidu sun bayyana cewa masu farmakin sun shige gidaje daga a jere a jere suna aiki har tsawon awanni kafin su gudu zuwa dajin da ke kusa da su tare da waɗanda suka sace.

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kwamandan ‘Yan Sa-kai, Sun Jikkata Wasu A Katsina

Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro, ba su samu nasarar bin ƴan bindigar ba zuwa bayan iyakar garin. Shugaban ƙaramar hukumar Dandume, Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa adadin masu farmakin sun kai fiye da 100.

Musa ya nuna damuwa game da yadda hare-haren ke faruwa akai-akai, yana kira ga hukumomi su ƙara tsaurara matakan tsaro don kare al’ummomin da ke cikin hatsari. Hukumomin tsaro na Jihar Katsina har kawo yanzu ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba game da lamarin ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gaza: Isra’ila ta kashe Falasindawa 58 a awa 58
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina
  • Sharhin Bayan Labarai: Zanga-Zanga A Kasashen Larabawa Ta Goyon Bayan Falasdinaw A Gaza
  • Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi
  • Gaza : adadin ‘yan jaridar da aka kashe ya haura 210
  • Hamas Ta Yaba Da Ma’aikaciyar Kamfanin Microsoft Wacce Ta Fallasa Yadda Kamfanin Yake Taimakawa HKI
  • Araqchi: Iran ba ta da matsala game da tattaunawa amma ba za ta lamunci yi mata barazana ba
  • An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36
  • Francesca Albanze: Abinda Yake Faruwa A Gaza Kisan Kiyashi Ne
  •  Kungiyar Malaman Musulunci Ta  Duniya Ta  Yi Fatawar Wajabcin Taimakawa Falasdinawa