Aminiya:
2025-04-08@20:30:46 GMT

WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta

Published: 8th, March 2025 GMT

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Nijeriya a ƙarshen makon nan.

Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba.

Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya

Kakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya.

Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin shigar da maganin cikin ƙasar akan lokaci, kuma a watan Janairu aka amince da hakan.

Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da rahoton samun aƙalla mutum 1,000 da cutar kuturta a duk shekara, wadda cuta ce da ke kama fatar jiki da jijiyoyi da idanu.

Ana iya magance cutar bayan shan magani na wani lokaci, amma idan ba a shan magani, cutar na ƙaruwa, idan take jawo gyambo da kuma nakasa kamar makanta da shanyewar rabin jiki.

Haka kuma, masu fama da cutar na fuskantar hantara da tsangwama a cikin al’umma.

Sai dai magungunan da Nijeriya take da su na cutar sun ƙare a farkon shekarar 2024 sakamakon jinkirin da aka samu na sabbin dokokin cikin gida da aka samar na gwaje-gwaje kan magungunan da ake shigar da su cikin ƙasar.

Jinkirin wanda ya jawo wahalhalu a Nijeriya, misali ɗaya ne daga ake samu a tsarin duniya wanda ke faruwa a ƙasashe da dama waɗanda suka haɗa da Indiya da Brazil da Indonesia a ‘yan shekarun nan, kamar yadda wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya kan cutar kuturta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ƙididdigar WHO ta nuna cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 12 da ke bayar da rahoton kamuwa da cutar inda ake samun tsakanin mutum 1,000 zuwa 10,000 a duk shekara masu kamuwa cutar, bayan Brazil, Indiya da Indonesia.

Kowace ƙasa tana buƙatar allurai na kuturta, wanda magani ne na kafso da ake amfani da shi na tsawon watanni 12, daga WHO kowace shekara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nijeriya cutar kuturta

এছাড়াও পড়ুন:

An Samu Karuwar Tafiye Tafiye Zuwa Ketare Yayin Hutun Bikin Qingming Na Sin

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lakurawa Sun Kashe ’Yan Sa-kai 13 A Wani Sabon Hari A Kebbi
  • An Buɗe Sabbin Cibiyoyin Kula Da Masu Cutar Sankarau A Jihohi 6
  • An Samu Karuwar Tafiye Tafiye Zuwa Ketare Yayin Hutun Bikin Qingming Na Sin
  • Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC
  • JMI Ta Kaddamarda Sabbin Ci Gaban Da Ta Samu Da Fasahar Nukliya A Ranar Makamashin Nukliya Ta Kasar
  • Arzikin Nijeriya Ya Habaka Zuwa Naira Tiriliyan 22.61 A Zangon Karshe Na 2024 – CBN
  • Kofin Duniya 2026: Kasashen Da Suka Samu Tikitin Shiga Gasar Zuwa Yanzu
  • An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36
  • Duk Da Matsin Tattalin Arziki, Bukukuwan Sallar Bana Ta Yi Armashi
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya