Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
Published: 8th, March 2025 GMT
Yanzu haka adadin matan kasar Sin mamallaka sana’o’i na ta karuwa sannu a hankali, inda ya zuwa yanzu mata ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai inganci a kasar.
Wasu alkaluma daga hukumar lura da hada hadar kasuwanni ta kasar sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, adadin kamfanoni da matan kasar Sin suka zuba jari sun haura miliyan 23, adadin da ya kai kaso 41.
Alkaluman sun nuna adadin hada-hadar kamfanoni masu jarin matan kasar Sin na ta karuwa, da kimanin kaso 9.8 bisa dari a duk shekara tun daga shekarar 2012, a gabar da karin mata ke kafawa, da zuba jari a kamfanoni daban daban. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya.
Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.