Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara.

 

“Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara.

Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka.

 

“Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.”

 

Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da ke aiwatar da sauye-sauye na tattalin arziki da zamantakewa tana fuskantar ƙalubale, amma ya jaddada cewa tsare-tsaren Shugaban Ƙasa Tinubu sun taimaka wajen rage wahalar da ke tattare da irin waɗannan sauye-sauye.

 

Ya ce: “Kowace ƙasa da ta aiwatar da wani sauyi na zamantakewa da tattalin arziki tana fuskantar matsaloli a farkon tafiya, amma ina ganin cewa a Nijeriya, an rage tsawon wannan lokaci saboda hangen nesa, jajircewa, da ƙarfin gwiwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke da shi cewa wannan gyara zai kai Nijeriya ga ci gaba mai ɗorewa.”

 

Idris ya bayyana Faransa a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗar Nijeriya kuma ya buƙaci gwamnatin Faransa da ta mara wa shirin gyaran tattalin arzikin Tinubu baya domin ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

 

Har ila yau, ya jinjina wa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, bisa girmamawar da ya yi wa Shugaban Ƙasa Tinubu ta gayyata zuwa ziyarar gwamnati a watan Nuwamba 2024, yana mai cewa irin wannan girmamawa ba kasafai ake yi wa shugabanni ita ba.

 

Ministan ya tabbatar wa jakaden na Faransa cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiwatar da duk yarjejeniyoyin da ta ƙulla da gwamnatin Faransa a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu.

 

Haka kuma, Idris ya yaba wa Jakada Fonbaustier bisa ƙoƙarin sa na inganta hulɗar Nijeriya da Faransa tun daga lokacin da aka naɗa shi.

 

A nasa jawabin, Jakada Fonbaustier ya ce ziyarar sa ta ƙunshi ƙirƙirar hanyoyin aiwatar da yarjejeniyoyin da Shugabannin ƙasashen biyu suka cimma a lokacin ziyarar Shugaban Ƙasa Tinubu a Faransa a bara.

 

Ya bayyana ƙudirin gwamnatin Faransa na tallafa wa Nijeriya wajen inganta hanyoyin sadarwa da fasahar yaɗa labarai.

 

Ya ce: “Dole ne mu tabbatar da cewa an yi aiki tuƙuru don bin diddigin ziyarar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a birnin Paris a watan Nuwamba.

 

“Shugabannin biyu sun tsara wata sabuwar hanya mai faɗi don haɓaka dangantaka, kuma a wannan fanni, sadarwa da watsa labarai suna da matuƙar muhimmanci.

 

‘A nan ne Faransa za ta iya bayar da gudunmawa ta fuskar ƙwarewa da fasaha.”

 

Jakaden ya bayyana Minista Idris a matsayin gwarzon sauyi a fannin sadarwa a Nijeriya, yana mai cewa matsayin sa a gwamnatin Tinubu ya dace da inganta matsayin Nijeriya a idon duniya da kuma janyo hannun jari daga ‘yan kasuwar Faransa da za su hallara a Paris a ranar 10 ga Afrilu, 2025, don Taron Kasuwanci na Faransa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa Tinubu da Shugaban Ƙasa

এছাড়াও পড়ুন:

Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar

Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala.

Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci,  har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa.

Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin.

A ranar lahadin da ta gabata ce hukumar zaben kasar Gabaon ta bada sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a ranar Asabar wanda ya nuna cewa masu zabe a kasar sun zabi Brice a matsayin shugaban kasa tare da samun kasha 90.4% na yawan kuri’un da aka kada, kuma yawan mutanen da suka fito kara kuri’un ya kai kasha 74%.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC
  • Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
  •  Aljeriya Ta Kori Jami’an Diflomasiyya Faransa 12
  • Yaƙin Neman Zaɓe A 2027: Ƙungiya Ta Nemi A Maye Gurbin Mai Magana Da Yawun Shugaban Ƙasa
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
  • Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • Inganta Rayuwar Al’umma: Amurka Da Ƙungiyar Kasuwanci Ta Nijeriya Sun Karrama Gwamna Lawal
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu