Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1]
Published: 9th, March 2025 GMT
SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1 BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 1
Sharhi:
Shehun malami Ibnu Juzai (Allah ya yi masa rahama) yana bayani a nan game da ma’anar Tafsiri, wanda ke nufin fassara da ƙarin bayani kan ma’anonin ayoyin Alƙur’ani. A bisa wannan magana, ana iya fahimtar cewa:
1. Tafsiri yana nufin bayani da sharhi na Alƙur’ani – Wato fassara da bayanin ma’anar ayoyi domin su fi zama a fili ga masu karatu da sauraro, don su fahimci saƙon da ke cikinsu.
2. Tafsiri yana bayyana ma’anar ayoyi dalla-dalla – Manufarsa ita ce kawar da ruɗani da kuma hana kuskuren fahimta.
3. Hanyoyin bayani a tafsiri suna da matakai daban-daban:
Ta lafazin ayar kai tsaye (بِنَصِّهِ) – Wato bayani a fili kamar yadda ayar take, ba tare da ƙarin sharhi ba.
Ta hanyar alama da ishara (إِشَارَتِهِ) – Wato fahimtar ma’anar da ke ƙunshe a tsarin ayar, sigar kalmomi, ko wasu dalilan shari’a da suke cikinta.
Ta fahimtar abin da ayar ke iya nufi (مُحْتَمَلِهِ) – Wannan yana buƙatar zurfin nazari, domin fahimtar ma’anar da za a iya ɗaukowa daga ayar bisa dalilai masu goyon baya.
Daga wannan bayani, ana iya fahimta cewa tafsiri ba wai kawai fassara ne kai tsaye ba, har da zurfafa fahimta ta hanyoyi daban-daban, tare da la’akari da sauran dalilan shari’a. Wannan yana taimakawa wajen fahimtar saƙon da Allah yake isarwa ta cikin Alƙur’ani cikin ingantacciyar hanya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki
এছাড়াও পড়ুন:
Ya lakada wa ’yarsa duka har lahira
Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas.
Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu.
Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu.
Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi.
Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayu