Senegal, Ta Karbi Wasu Sansanonin Sojin Faransa A Kasar
Published: 9th, March 2025 GMT
Senegal ta karbi wasu sansanonin soja na faransa a kasar a wani bangare na janye sojojin faransar daga kasar ta Yammacin Afirka.
Ofishin jakadancin Faransa a Dakar ya sanar da cewa an mika wurare da gidaje a yankunan Marechal da Saint-Exupery na Dakar ga hannun gwamnatin Senegal.
Sauran kuma “za a mika su ne kamar yadda bangarorin biyu suka amince da jadawalin da suka sanya wa hannu”.
A ranar 12 ga Fabrairu Faransa ta sanar cewa ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa da Senegal da zai shirya tsare-tsaren ficewar sojojin Faransa da kuma mika sansanonin zuwa karshen shekarar nan.
“Kwamitin ya kuma kaddamar da aikin yin garen-bawul ga hadakar tsaro,” a cewar sanarwar.
A watan Nuwamban 2024 ne Shugaba Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zabe bisa akidar kawo sauyi, ya bayyana cewa duka sojojin Faransa da na kasashen waje za su fita daga Senegal zuwa karshen 2025.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.