Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu.

Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.

Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu.

Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati.

Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da matukar damuwa game da sha’anin ilimi da kundin tsarin mulkin Amurka kan ‘yancin fadin albarkacin baki.

Dama Trump ya sake nanata barazanarsa a wannan makon, inda ya yi alkawarin rage kudaden da ake ba duk jami’ar da ta ba da damar gudanar da zanga-zanga ba bisa ka’ida ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci.

An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6

Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan.

Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba.

Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za ta ci gaba da wakiltar al’ummarta.

A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce: “Dakatar da ni ba bisa ƙa’ida ba ya saɓa wa adalci da gaskiya.

“Ba zai karɓe min matsayin da ’yan Kogi suka ba ni ba. Zan ci gaba da yi wa mutanena da ƙasata hidima har zuwa 2027—da ma bayan hakan.”

Majalisar ta dakatar da ita na tsawon watanni shida bayan karɓar shawarar kwamitin Ladabtarwa.

Matakin dai ya haifar da zazzafar muhawara s tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin an tauye mata haƙƙinta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Birtaniya: Wani Mutum Ya Hau Kan Hasumayar Agogon “Big  Bang” Dauke Da Tutar Falasdinu
  • Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe
  • Qatar Ta Ce Bata Goyon Bayan Yakin Don Warware Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • FUD Ta Nada Abdullahi Yahaya Bello Daraktan Hulda da Jama’a
  • OIC Ta Yi Maraba Da Shirin Gwamnatocin Larabawa Na Sake Gina Zirin Gaza
  • An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a Kebbi
  • Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi
  • Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha
  • Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya