HausaTv:
2025-04-09@00:06:03 GMT

Jamus, Faransa, Birtaniya Da Italiya Sun Yi Maraba Da Shirin Larabawa Kan Gaza

Published: 9th, March 2025 GMT

Kasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Italiya “sun yi maraba” da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza.

 A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen suka fitar a birnin Berlin, sun ce shirin idan an aiwatar da shi zai bada damar gaggauta warware mummunan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza.

A yayin taron da suka gudanar ne a ranar Talata data gabata a Masar kasashen Larabawan suka gabatar da wani shiri da zai lakume dalar Amurka Biliyan 53 na sake gina Gaza cikin fiye da shekara biyar inda shirin zai mayar da hankali kan taimakon gaggawa,dawo da ababen more rayuwa da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Shirin na kasashen Larabawa tamakar neman maye gurbin shirin da shugaban Amurka Donald Trump, ya fitar a watan da ya gabatar na karbe iko da zirin Gaza dama tilasta musu hijira zuwa kasashen Masar da Jordan.

Matakin na Trump dai ya fuskanci martini da tofin Allah tsine daga daga Falasdinawa da kasashen Larabawa da kuma gwamnatoci da yawa a duniya, inda sukayi fatali da duk wani shiri na korar mutanen Gaza daga kasarsu ta asali.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa

এছাড়াও পড়ুন:

 Kasashen Iran, Rasha Da China Za Su Yi Taro A Moscow Domin Tattauna Batutuwa Da Dama

 Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha.

Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a.

A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Faransa, Masar da Jordan sun yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza
  • An sake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv
  • NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu
  • Kasar Sin Na Shirin Gaggauta Karfafa Karfinta A Bangaren Aikin Gona
  • Sharhin Bayan Labarai: Zanga-Zanga A Kasashen Larabawa Ta Goyon Bayan Falasdinaw A Gaza
  •  Kasashen Faransa Masar Da Jordan Sun Yi Taro Akan Gaza
  •  Kasashen Iran, Rasha Da China Za Su Yi Taro A Moscow Domin Tattauna Batutuwa Da Dama
  • Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun kira jakadunsu daga Aljeriya
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi?
  • Burtaniya Ta Soki Gwamnatin Netanyahu Kan Hana ‘Yan Majalisarta Biyu Shiga Cikin Isra’ila