Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar.

Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.”

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.”

Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya kawai; A maimakon haka, suna amfani da shawarwari a matsayin “hanyar cimma manufofinsu” a fannoni kamar karfin tsaron Iran da karfin kasa da kasa, wadan ko shakka babu Iran za ta yi watsi dasu.

Ya kara da cewa, suna tabo batun tattaunawar ne domin matsa lamba kan ra’ayin jama’a, don haka Iran ta ki yin shawarwari da su, duk da cewa sun nuna a shirye su ke.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi

Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom.

Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu.

A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kalibaf: Maganar Donald Trump Akan Tattaunawa Da Iran Yaudara Ce
  • Masana A Iran Sun Samar Da Maganin Rashin Haihuwa Na Maza
  • Shawarwari Kan Kayyade Amfani Da Siga
  • Jagora: Iran, Tabbas Zata Ki Amincewa Da Tattaunawa Da Kasashe Masu Girman Kai
  • Oficin Jakadan Iran A MDD Ya Ce Babu Wani Sako Da Suka Karba Daga Shugaban Kasar Amurka
  • Fararen hula 162 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan a lardunan gabar tekun Syria
  • Gwamnati Ta Amince Da Bai Wa Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Lasisi
  •  Ayatullah Khatami: Tattaunawa Da Amurka Kaskanci  Ne
  • Iran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Birtaniya Na Cewa Tehran Na Barazana Ga Tsaron Kasar