An harbe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a Kwara
Published: 9th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin.
Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — RahotoMuhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi.
“A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan sanda sun zo sun fara bincike.”
Sai dai mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kwara, Ejire Adeyemi Toun da wakilinmu ya tuntuɓa, ta buƙaci ya ba ta lokaci za ta waiwaye shi daga baya.
Bayanai sun ce marigayin mai shekaru 32 tsohon hadimi ne a wurin Shugaban Ƙaramar Hukumar Moro kuma ɗaya daga cikin shugabannin Matasa Fulani a Jihar Kwara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alhaji Idris Abubakar Sakaina Jihar Kwara Ƙungiyar Miyetti Allah
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi
Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi.
Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.
HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDCWani mazauni, Malam Ibrahim Augue, ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ’yan sa-kai suka bi su.
“A nan suka yi wa ’yan sa-kan kwanton ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.”
Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.