A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin.

Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike kan al’amuran birnin Kudus, ya jaddada cewa, matakin da gwamnatin sahyoniyawa ta dauka na hana masu ibadar I’itikafi a cikin masallacin Al-Aqsa wani mataki ne na cin zarafi da kuma muzgunawa hakkokinsu na addini.

Ya kara da cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya suna amfani da hakan ne don shimfida ikonsu a kan masallacin Al-Aqsa, domin kuwa a shekara ta 2015 an ba da izinin yin I’itikafi a cikin wannan masallaci a duk ranakun watan Ramadan.

Hukumar bayar da agaji ta Musulunci a birnin Kudus ta sanar da cewa sama da masu ibada dubu 80 ne suka gudanar da sallar isha’i da tarawihi a harabar masallacin Al-Aqsa mai albarka a yammacin ranar Alhamis, wadanda akasarinsu mazauna birnin Kudus ne da yankunan da yahudawa suka mamaye a shekara ta 1948.

A daidai lokacin da watan Ramadan ya shiga, sojojin Isra’ila sun jibge dakaru masu yawa a birnin Kudus da kuma kewayen masallacin Al-Aqsa don hana Falasdinawa masu ibada shiga masallacin .

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gaza: Isra’ila ta kashe Falasindawa 58 a awa 58

Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula.

Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Ya lakada wa ’yarsa duka har lahira Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Yan Sanda A Saudiya Sun Tsare Wata Bafalasdinya Saboda Bayyana Tutar Kasarta A Kan Jakarta A Masallacin Ka’aba
  • Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58
  • Gaza: Isra’ila ta kashe Falasindawa 58 a awa 58
  • Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza
  • Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
  • Rahoto: Yara Falasdinawa 350 ne Isra’ila ke tsare da su a gidajen kurkuku
  • Gwamnatin Yobe Ta Ƙaryata Rahoton Bayyanar Boko Haram A Babban Birnin Jihar
  • Burtaniya Ta Soki Gwamnatin Netanyahu Kan Hana ‘Yan Majalisarta Biyu Shiga Cikin Isra’ila
  • Kanwan Katsina Ya Yabi Gwamnatin Katsina Kan Farfado Da Al’adar Hawan Durbar