Kasashen Turai sun goyi bayan shirin Larabawa na sake gina Gaza
Published: 9th, March 2025 GMT
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin.
Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka aiwatar da hakan cikin gaggawa.
A ranar Asabar ne kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC mai mambobi 57 ta amince da shawarar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a hukumance kan sake gina Gaza a wani taron gaggawa da ta gudanar a kasar Saudiyya.
OIC ta bukaci “kasashen duniya da cibiyoyin bayar da kudade na kasa da kasa da na shiyya-shiyya da su gaggauta ba da tallafin da ya dace ga shirin.”
Wani cikakken daftarin shirin sake gina Gaza da Masar ta gabatar ya hada da ware dala biliyan 53 don sake gina gina yankin, da kuma batun kafa kwamitin gudanarwa domin tafiyar da yankin zirin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa, Masar da Jordan sun yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza
Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin.
Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a Gaza kuma ya nuna damuwar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan tashe-tashen hankula da rikicin jin kai a Gaza.
Haka kuma sanarwar wadannan kasashe uku ta nuna muhimmancin hanyar diflomasiyya na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A baya dai shugaba Macron ya nuna adawarsa da mamaye yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta yi.
Macron ya kuma kira sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a yankin bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakiyar watan Maris da cewa wani babban koma baya ne.
Sarki Abdallah na biyu na Jordan, shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi na Masar sun bayyana cewa, “Dole ne a dakatar da yakin Gaza duba da bala’in da ya haifar a yanzu.
Tashin hankali, ta’addanci, da yaki ba za su iya samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba.
Sanarwar ta yi nuni da bukatar gaggawa na kara kai kayan agaji a Gaza, inda tuni aka fara samun matsalar yunwa, da kare hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ma’aikatan jin kai da ke aiki a yankin.