Iran, Rasha da China, sun fara wani atisayin sojojin ruwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar
Published: 9th, March 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku.
Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne mu kara karfinmu na yaki, inji sakataren tsron na Amurka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, kalaman da jami’in na Amurka ya yi suna haifar da sabani da kuma yada abin kasar Sin ke kallonsa a matsayin barazana ga kasarta.
Lin ya kara da cewa, “Muna kira ga Amurka da ta daina gina tunaninta akan masaniyarta dangane da Sin a lokutan baya, musamman lokacin yakin cacar baki, domin kuwa a yanzu Sin ba wadda Amurka ta san ice a lokutan baya ba.
Sakataren tsaron Amurka ya fada a wata hira da kafar yada labarai ta Fox News a ranar Larabar da ta gabata cewa, Amurka ta shirya tsaf domin shiga kowane irin yaki a duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata
Duk da matsin lambar da Amurka ke yi, kasar Sin tana da dabararta, za ta ci gaba da mai da hankali kan ayyukanta, za ta kuma rika bude kofarta ga ketare. Har kullum kasar Sin na ganin cewa, ainihin huldar da ke tsakaninta da Amurka ita ce samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare. Ya kamata a daidaita sabanin ciniki ta hanyar tattaunawa cikin adalci. Amma idan Amurka ta fara dora harajin da ta yi shelar dauka, to, kasar Sin za ta dauki wajibabbun matakai, domin kiyaye halastattun hakkokinta. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp