Isyaku Mahmud, makaho ne dan shekara 28 da ke sana’ar sayar da data a yankin Kudancin Kaduna.
Ya shaida wa Aminiya cewa har sana’ar hada-hadar kudi ta POS yana yi a baya, amma yanzu ba shi da jari.
Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufaiAminiya ta ga yadda makahon yake sarrafa manhajojin WhatsApp is Fesbuk kuma yake sayar da data kai tsaye daga wayarsa ta hanyar amfani da tsarin Smart Cash tare da tura kudi da wayar tasa, kamar yadda ya gwadawa wakilinmu.
Dan asalin garin Yalwa da ke Karamar Hukumar Tudun Wada (Dan Kadai) da ke Jihar Kano ne, ya kwashe shekaru kusan biyar yana zuwa yawon bara a garin Kafanchan da ke Jihar Kaduna.
Aminiya ta samu zantawa da shi, inda ya gwada duk abubuwan da yake yi da wayarsa ciki, har da lalubo wakar da ya yi ya kuma tura cikin wani zaure na mawaƙa ba tare da wani ya nuna masa ko ya taimaka ba.
Yana iya kuma tattaunawa da kowa ta hanyar sauti a manhajar WhatsApp tunda bai iya rubutu ba.
Amma da kansa yake budewa ya lalubo wanda yake son tura wa da sako kuma ya tura masa.
“Ka san ina yin wakokin yabon Manzon Allah. Idan na samu ƙarin baitin sai na ɗauko wayata na rera tunda ba zan iya rubutawa ba.
“Idan na gama hada adadin baitukan da nake so akwai dalibai ’yan Islamiyya, sai na ba su muje inda ake buga wakoki a studiyo, sai su hau su rera.
“Ba ni nake rerawa ba, amma duka wakokina ne. A can garinmu nake wannan kuma a yanzu haka ina da kasidu da aka buga sun haura guda 20.
“An haife ni ne a shekarar 1997, an shaida min cewa an haife ni da idanu na garai, amma bayan an yaye ni, a shekarar sai mahaifiyata ta rasu kuma tun daga nan sai na daina gani, wato na makance, shine har zuwa yau kuma,” in ji shi.
Ya ce ya yi karatun tsangaya kafin daga baya aka matsa masa cewa sai ya fita yawon bara.
“Saboda haka ba a son raina nake bara ba, amma a lokacin babu wani abu da zan iya yi. Wannan ya faru ne a shekarar 2012 tun lokacin nake bara.”
Ya ce da zai samu wani tallafi na jari, a shirye yake ya yi wasu sana’o’i ko buɗe shagon harkar POS ko wani abu da zai iya dogaro da shi musamman yanzu da yake da yara ƙananan guda biyu da yake son su samu kulawa ta musamman tare da yin karatu mai zurfi.
“Ina da mata daya da ƙananan yara guda biyu kuma gaskiya ina son su yi karatu duka na addini da na boko.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Nijeriya a ƙarshen makon nan.
Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba.
Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a NijeriyaKakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya.
Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin shigar da maganin cikin ƙasar akan lokaci, kuma a watan Janairu aka amince da hakan.
Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da rahoton samun aƙalla mutum 1,000 da cutar kuturta a duk shekara, wadda cuta ce da ke kama fatar jiki da jijiyoyi da idanu.
Ana iya magance cutar bayan shan magani na wani lokaci, amma idan ba a shan magani, cutar na ƙaruwa, idan take jawo gyambo da kuma nakasa kamar makanta da shanyewar rabin jiki.
Haka kuma, masu fama da cutar na fuskantar hantara da tsangwama a cikin al’umma.
Sai dai magungunan da Nijeriya take da su na cutar sun ƙare a farkon shekarar 2024 sakamakon jinkirin da aka samu na sabbin dokokin cikin gida da aka samar na gwaje-gwaje kan magungunan da ake shigar da su cikin ƙasar.
Jinkirin wanda ya jawo wahalhalu a Nijeriya, misali ɗaya ne daga ake samu a tsarin duniya wanda ke faruwa a ƙasashe da dama waɗanda suka haɗa da Indiya da Brazil da Indonesia a ‘yan shekarun nan, kamar yadda wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya kan cutar kuturta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ƙididdigar WHO ta nuna cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 12 da ke bayar da rahoton kamuwa da cutar inda ake samun tsakanin mutum 1,000 zuwa 10,000 a duk shekara masu kamuwa cutar, bayan Brazil, Indiya da Indonesia.
Kowace ƙasa tana buƙatar allurai na kuturta, wanda magani ne na kafso da ake amfani da shi na tsawon watanni 12, daga WHO kowace shekara.