Aminiya:
2025-04-10@14:54:19 GMT

An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba

Published: 9th, March 2025 GMT

Wata kotu a Birnin Paris na Ƙasar Faransa, ta samu tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Faransa, Bernard Squarcini, da laifin zamba da amfani da dukiyar jama’a ba bisa ƙa’ida ba.

Squarcini, mai shekaru 69, ya jagoranci hukumar tsaron cikin gida ta Faransa daga 2008 zuwa 2012.

Makahon da ke sana’ar POS Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto

Bayan ya bar aiki, kamfanin LVMH ya ɗauke shi aiki a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin tsaro.

A ranar Juma’a da ta gabata, kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari, inda biyu daga ciki aka dakatar da su.

An same shi da laifin amfani da abokan tsaronsa don cimma burinsa, har da samun bayanan sirri na kamfanin LVMH.

Za a ba Squarcini damar yin zaman gidansa, amma sanye da munduwa ta lantarki.

Haka kuma, an ci shi tarar Yuro 200,000 tare da dakatar da shi daga duk wani aiki da ya shafi leƙen asiri ko bayar da shawara na tsawon shekaru biyar.

Lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka kara kan hukuncin.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa Tsohon Shugaban Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar

Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar.

Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.

Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a ƙasar har ya wuce lokacin da keɓe, to ko shakka babu ya saɓa ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

Mahukuntan sun buƙaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da waɗannan lokuta da aka ƙayyade.

An kuma yi gargaɗin cewa duk wani jinkiri na barin mutane, ƙasar za a ɗauke shi kamar karya doka.

Ta ce duk kamfanin da aka samu da ƙin bayyana mutanen da suka ƙi koma wa ƙasashensu to za a ci tararsu riyal dubu 100.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima
  • Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki NUPRC — Buba Galadima
  • Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
  • Barcelona Ta Kama Hanyar Lashe Gasar Zakarun Turai A Karon Farko Bayan Shekaru 10
  • Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Bita Ga Alhazai
  • Saudiyya ta bayar da wa’adin ficewar dukkanin masu aikin Umrah daga kasar
  • Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar
  • Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
  • Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza