Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shirye daga Lebanon ta ambaci cewa; Wasu kauyuka na mabiya mazhabar Alawiyya dake Tartus, da kuma Lazikiyya, sun fuskanci hare-hare daga masu dauke da makamai.

A yau Lahadi, masu dauke da makaman sun kutsa cikin wasu kauyukan Ramilah, Naq’a dake kusa da Jabalah.

Daga jiya zuwa yau masu dauke da makaman sun yi kisan kiyashi a wurare  fiye da 10.

Majiyar Almayadin ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda aka kashe bisa bangaranci sun kai 1000.

Sai dai kuma tshohon mai bai wa shugaban majalisar ‘yan Alawiyya shawara Muhammad Nasir, ya ce, adadin wadanda aka kashe din sun kai 1,700.

Hare-haren sun hada da kona kauyuka 6 a yankin gabar ruwan Midtreniya na kasar Syria.

Da akwai wasu daruruwan gawawwaki a kwance akan titunan garuruwa da kauyuka da biranen yakin Lazikiyya da Hasakah.

A cikin wasu kauyukan mutane da dama sun gudu zuwa kan duwatsu da dajuka domin su tsira da rayukansu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su.

Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa

Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa akwai ƙaninsa Ishaya Kukah na cikin waɗanda aka kama.

“Yayana Ishaya, shi kaɗai ne namiji a cikin waɗanda aka sace; sauran mata da yara ne, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare,” in ji shi.

Kukah ya ƙara da cewa har ya zuwa lokacin da yake zantawa da wakilinmu, babu wata tuntuɓa da masu garkuwar suka yi dangane da neman kuɗin fansa.

“Muna yi musu addu’ar Allah ya kare su yayin da muke jiran kowane kira,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an dawo da waɗanda lamarin ya rutsa da su lafiya, yana mai jaddada cewa galibin waɗanda aka sace mutane ne masu rauni.

Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi wa wakilinmu ƙarin bayani kan lamarin, amma har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ba.

Mazauna yankin na ci gaba da yin kira da a tsaurara matakan tsaro domin daƙile matsalar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Birtaniya: Wani Mutum Ya Hau Kan Hasumayar Agogon “Big  Bang” Dauke Da Tutar Falasdinu
  • Mutane 1,018 ne aka kashe a ci gaba da kisan kiyashi kan tsiraru a gabar tekun Syria
  • Tashe-tashen Hankula Na Ci Gaba Da Yin Sanadin Rayuka A Siriya
  • Aragchi: Hare-hare Kan Cibiyoyin Makamashin Nukliya Na Kasar Iran Ba Za Su Wargaza Shirin Ba
  • Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (2)
  • Al-Houthi: Mun Baiwa Isra’ila Wa’adin Kwanaki 4 Da Ta Kawo Karshen Killace Gaza
  • Fararen hula 162 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan a lardunan gabar tekun Syria
  • An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
  • An Ayyana Dokar Ta-baci A Wasu Yankunan Siriya