Kalibaf: Maganar Donald Trump Akan Tattaunawa Da Iran Yaudara Ce
Published: 9th, March 2025 GMT
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana.
Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta.
A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa.
Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi mu’amala da sauran kasashe, yana tabbatar da cewa managarsa akan tattaunawa yaudara ce, da kuma son raba Iran da karfin da take da shi, ta hanyar sanya ta ja da baya akan wasu tsare-tsarenta na tsaro.
A cikin kwanakin nan ne dai Donald Trump ya yi batun aikewa da Iran sako yana kiranta zuwa tattaunawa, lamarin da Tehran ta kore.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya.
Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.