Sa’adatu Ali JC ta raba wa mata 150 injinan markaɗe a Gombe
Published: 9th, March 2025 GMT
A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai.
Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata su samu sana’a da za ta rage musu dogaro da wasu.
“Wannan tallafi yana da muhimmanci domin zai taimaka wa mata su kula da kansu da iyalansu ba tare da jira komai daga mazajensu ba.
“Wannan kuma wani yunƙuri ne na taimakon jama’a kamar yadda maigidana, Hon. Ali Isa JC, ke yi a kodayaushe,” in ji ta.
Ta bayyana cewa mijinta ya tallafa wa mutum sama da 2,000 da kayan abinci da na noman rani don rage yunwa a cikin al’umma.
Haka kuma, ta taɓa koyawa wasu mata sana’ar yin takalma, wanda har takalmansu ke zuwa ƙasashen waje saboda ingancinsu.
Hajiya Sa’adatu ta ja hankalin matan da suka amfana da injinan da ka da su sayar da su, sai dai su yi amfani da su don amfanin kansu da iyalansu.
“Idan kuka yi amfani da wannan tallafi yadda ya kamata, zai zamo muku wata babbar hanya ta samun riba kamar yadda waɗanda suka koyi sana’ar takalma suka samu nasara,” inji ta.
Sannan ta yi kira ga masu hali da su taimaka wa jama’a, ba sai ‘yan siyasa kaɗai ba, domin hakan zai rage zaman banza da talauci a cikin al’umma.
Wasu daga cikin matan da suka amfana sun jinjina mata, inda suka ce ta zama abin koyi a cikin mata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗan Majalisa Injinan Markaɗe Matar Ali JC Rage Talauci
এছাড়াও পড়ুন:
Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wasu mutum huɗu da take zargi ’yan bindiga ne da tarin makamai da kuɗaɗe a hannunsu.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke ababen zargin ne a ranar 6 ga wannan wata na Maris.
NMDPRA ta ba da lasisin gina sabbin matatun mai 3 a Nijeriya Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar DattawaSP Kiyawa ya ce an kama ababen zargin ne da kimanin naira 1,028,800 a gidan mai na Chula da ke unguwar Hotoro suna ƙoƙarin sayen bindigar AK-47.
Sanarwar ta ce an samu mutanen huɗu waɗanda dukkansu matasa ne da wasu ƙananan bindigogi ƙirar gida, da wuƙaƙe da adduna da wayoyin hannu da wasu layu.
Ya bayar da sunayen matasan da ke hannu da suka haɗa da — Shukurana Salihu mai shekaru 25 da Rabi’u Dahiru mai shekaru 35 da Ya’u Idris mai shekaru 30 duk daga Jihar Katsina sai kuma Muktar Sani mai shekaru 30 daga yankin ’Yandodo na unguwar Hotoro da ke Kano.
SP Kiyawa ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan ababen zargin da ke tsare a sashen binciken miyagun laifuka na hedikwatarsu da ke Bompoi.
Rundunar ’yan sandan wadda ta ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike, ta kuma jaddada ƙudirinta na kawo ƙarshen duk wasu miyagu a faɗin jihar.
Ta kuma miƙa godiya ga al’umma dangane da goyon baya da haɗin kan da take samu a ƙoƙarinta na yaƙi da masu tayar da zaune tsaye.