Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen.

Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan  fararen hula da rana tsaka.

Tun bayan da gamayyar kungiyoyi masu dauke da makamai karkashin inuwar kungiyar Tahrir Sham mai alaka da kungiyar alkaida suka hambarar da gwamnatin Bashar Assad, suka fara aiwatar da kisa a bainar jama’a a kan tsiraru, bisa zargin cewa suna dad a alaka da gwamnatin Assad, amma lamarin ya kara tsanata a cikin ‘yan kwanakin nan.

Sakamakon tashin hankalin, an kashe ‘yan kasar Syria sama da 1,018, wadanda akasarinsu fararen hula ne, da suka hada da mata da kananan yara, a cewar wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta fitar, amma wasu bayanai daga bakunan mazauna yankunan da abin ya faru na nuni da cewa adadin ya zarta haka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

ACF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Kawo Karshe Tashe-Tashen Hankula Filato

Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato.

Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato.

ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada kai da al’ummomin yankin domin dakile barazanar tsaro.

Haka kuma, kungiyar ta nemi gwamnati ta kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma kama wadanda ke da hannu a ta’asar.

Kungiyar ta jaddada bukatar wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato tare da bukatar a hada kai da shugabannin gargajiya, dattawa, kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile lamarin.

ACF ta kuma bukaci al’umma su rika bai wa jami’an tsaro bayanai kan duk wani abu da ka iya kawo matsala.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Harajin China da Amurka: Mece ce makomar tattalin arziƙin duniya?
  • Harajin China da Amurka: Mene ne makomar tattalin arziƙin duniya?
  • Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi
  • Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayu
  • Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
  • Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun kira jakadunsu daga Aljeriya
  • Hassan Fadlallah: Amurka ke da alhakin ayyukan wuce gona da iri na Isr’aila a Lebanon
  • ACF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Kawo Karshe Tashe-Tashen Hankula Filato