HausaTv:
2025-03-10@09:46:28 GMT

Alummomin duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kisan fararen hula a Siriya

Published: 10th, March 2025 GMT

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu iyalai baki daya a wannan tashin hankali, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin “mai matukar tayar da hankali”.

Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan kisan kiyashin da masu dauke da makamai suka aikata, tare da hukunta wadanda suka aikata laifukan.

Babban jami’in kare hakkin bil adama na MDD ya kara da cewa, “Muna samun rahotanni masu matukar tayar da hankali kan yadda ake kashe iyalai baki daya, da suka hada da mata da yara,  yana mai jaddada kira a kan dole ne a daina kashe fararen hula a yankunan gabar teku a arewa maso yammacin Syria.

Ya yi kira da a gudanar da bincike na gaskiya cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba, kan dukkan kashe-kashe da sauran cin zarafin da aka aikata, ya kara da cewa “wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata hakan bisa ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar lafiya ta duniya ya bayyana fadan a matsayin abin damuwa sosai tare da tabbatar da cewa hakan yana yin mummunar  illa ga lafiyar mutane kai tsaye, domin kuwa a rusa cibiyoyin lafiya da motocin daukar marasa lafiya.

Tedros Adhanom ya wallafa cewa, “WHO tana aiki tukuru don isar da magunguna cikin gaggawa, don kulawa ta gaggawa ga wadanda suka jikkata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Kashe Mutum Akalla 70 A Yaki Tsakanin HKS Da Yan Tawaye A Kudancin Kasar Siriya

An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar.

Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a.

SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a. Ta kuma kara da cewa. a bakin ruwan garin Jabbeh kusa da lardin lardin lantaki mutane 48 aka kashe.

Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a cikin watan Desemban da ya gabata.

Labarin ya kara da cewa an kashe sojojin HTS akalla 16 a fafatawar jiya Alhamis, a bakin tekun Medeteranian a cikin lardin Lantakiya, inda Alawiyawa da musulmi mabiya mazhabar shia suka fi yawa a kasar.

A wannan yankin ne sansanin sojojin kasar Rasha suke ayyukansu a bakin ruwan Medeteranian. Alawiyawa sun aikwa sakonni a shafin Facebook inda suke bayyana cewa ta yaya, gwamnatin HTS zata yi amfani da hare-haren jiragen yakin helkomta a kansu bayan sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman hakkinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Majalisar Dinkin Duniya na rangadi a wuraren da aka aikata kisan kiyashi a Syria
  • Mutane 1,018 ne aka kashe a ci gaba da kisan kiyashi kan tsiraru a gabar tekun Syria
  • Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto
  • Tashe-tashen Hankula Na Ci Gaba Da Yin Sanadin Rayuka A Siriya
  • A ranar Mata Ta Duniya, Hamas Ta Yi Allawadai Da Kashe Mata 12,000 A Gaza
  • Fararen hula 162 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan a lardunan gabar tekun Syria
  • Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai
  • Wang Yi: Diflomasiyyar Kasar Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankalin Da Ake Bukata A Duniya Mai Cike Da Rikici
  • An Kashe Mutum Akalla 70 A Yaki Tsakanin HKS Da Yan Tawaye A Kudancin Kasar Siriya