Sheikh Qassem: Duk da wahalhalun, Hizbullah tana da karfinta
Published: 10th, March 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa.
A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa.
Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.”
Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta hanyar gwagwarmaya da ayyukan soji.
Shugaban na Hizbullah ya yi nuni da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Lebanon a fili take, babu wata boyayyiyar yarjejeniya da aka kulla, komai a bayyane yake.
Ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar ta yi magana karara a kan “kudancin kogin Litani” sau biyar, yana mai cewa, “Wannan shi ne tsarin da ya kamata mu bi.”
“Wannan yarjejeniya wani bangare ne na kuduri mai lamba 1701 na Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da ta’addancin Isra’ila,” in ji shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back
Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.
“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.
Sai dai duk da wannan gargaɗi, ƙungiyar ta Take It Back ta ce tana nan kan bakarta domin nuna adawa kan abin da ta kira mulkin kama karya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi a ƙasar nan.