Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa.

Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran  a matsayin tushen rashin tsaro a yankin.

Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba neman kera makaman nukiliya ba.

Shugaba Pezeshkian ya ce Iran ta ba da hadin kai kuma za ta ci gaba da hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA domin kara tabbatar wa duniya da cewa shirinta na ayyukan farar hula ne, sabanin abin da makiyanta suke yadawa..

A nasa bangaren Firaministan Norway ya ce, kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako da nufin warware matsalolin da ke faruwa a yankin yammacin Asiya a cikin lumana, tare da kara karfafa alakarta da kasar Iran.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya

Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu  tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai.

Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran kan cewa, babu hanyar da ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran sai hanyar Diblomasiyya.

Ya kumakara dacewa kungiyar tana maraba da duk wani ci gaba a wannan bangharen. Mai maganan ya kara da cewa wakilin EU a MDD ya yi wannan bayanin a gaban kwamitin tsaro na MDD a yan kwanakin da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sharhin Bayan Labarai: Yakin Kasuwanci Tsakanin Amurka da Kasashen Duniya
  • Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Harajin China da Amurka: Mece ce makomar tattalin arziƙin duniya?
  • Harajin China da Amurka: Mene ne makomar tattalin arziƙin duniya?
  • Limamin Pangu Gari Ya Nemi Gwamnan Neja Ya Sanya Baki Kan Rikicin Fili A Yankin
  • Li Qiang Ya Tattauna Da Shugabar Kwamitin EU
  • HKI Ta Kara Yawan Hare-Hare A Kan Gaza A Dai Dai Lokacinda Ake Kiranta Zuwa Tsagaita Wuta
  • Pezeshkian: Dole ne Amurka ta tabbatar da cewa da gaske take yi a game da tattaunawa
  • Kasar Sin Ta Nanata Kudurinta Na Ci Gaba Da Bude Kofa Yayin Wani Taro Da Kamfanonin Amurka 
  •  Kasashen Iran, Rasha Da China Za Su Yi Taro A Moscow Domin Tattauna Batutuwa Da Dama