Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci
Published: 10th, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) Sepp Blatter, da tsohon Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Turai (UEFA) Michel Platini, sun sake gurfana a gaban wata kotu a kasar Switzerland, domin sake duba tuhume-tuhumen da ake musu na cin hanci da rashawa.
Wata kotun daukaka kara ta musamman da ke zama a Muttenz ce ta saurari bukatar da ofishin babban mai shigar da kara na kasar ya kabatar, na sake dawo da tuhume-tuhumen da ake yi wa Blatter, wanda yake cika shekaru 89 a yau ranar 10 ga wannan wata na Maris, da kuma Platini mai shekaru 69.
Blatter, ya yi kokarin amfani da damar wajen wanke kansa, daga zargin cin hanci da aka yi musu da Platini, shahararren tsohon dan wasan Faransa.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a makon da ya gabata, Blatter ya bayyana shari’ar a matsayin bita-da-kulli, saboda kotun baya ta tabbatar da sahihancin kwantiragin da ke tsakaninsa da Platini.
Don haka ya ce ya na da tabbacin ita ma wannan kotun za ta tabbatar da hakan.
A shekarar 2022 ce dai kotu ta wanke su kan zargin cin hanci na dala miliyan 2 da dubu dari da ake musu, bayan shafe shekaru bakwai ana shari’ar.
Blatter dai ya jagoranci hukumar FIFA ne daga tsakanin shekarar 1998 zuwa 2015, inda aka sa ran Platini ya gajeshi a shugabancin hukumar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.