Aminiya:
2025-03-10@09:56:07 GMT

Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano

Published: 10th, March 2025 GMT

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi tsattsauran gargaɗi dangane da rahotannin da ke yawo kan cirar kuɗi daga albashin ma’aikatan gwamnati ko kuma ƙin biyan su gaba ɗaya.

Ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin ma’aikata da cin amanar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba.

Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi

Biyo bayan korafe-korafen da ma’aikata suka yi, na cewa wasu daga cikinsu sun shafe watanni ba tare da samun hakkokinsu ba, Gwamna Yusuf ya sha alwashin gano masu hannu a wannan ɗanyen aiki da kuma hukunta su.

“Gwamnatin nan ba za ta yarda da zalunci ma’aikatanta ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan mummunan aiki zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya kafa kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin matsalar, wanda zai gudanar da cikakken bincike kan tsarin biyan albashi daga watan Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025

An ɗora wa kwamitin alhakin gano ma’aikatan da abin ya shafa, tasirin hakan kan kuɗin gwamnati, tare da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Kwamitin, wanda ke da mambobi bakwai yana karkashin jagorancin Kwamishinan Raya Karkara da Ci-gaban Al’umma kuma tsohon Akanta Janar na Jiha, Abdulkadir Abdussalam.

Mambobin sun hada da: – Abdulkadir Abdussalam – Shugaban Kwamitin kuma Kwamishinan Raya Karkara da Ci-gaban Al’umma da Dokta Bashir Abdu Muzakkari – Mai ba da shawara na musamman kan tattalin arzikin zamani.

Sai Dokta Aliyu Isa Aliyu – Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano da Dokta Hamisu Sadi Ali – Darakta Janar na Hukumar Kula da Bashin Jihar Kano da Hajiya Zainab Abdulkadir – Darakta ta Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano.

Akwai kuma Aliyu Muhammad Sani – Darakta na Bincike da Tantancewa a Ofishin Sakataren Gwamnati da Ummulkulthum Ladan Kailani – Mataimakiyar Sakatariya, Ofishin Sakataren Gwamnati.

An bai wa kwamitin wa’adin kwanaki bakwai domin kammala binciken tare da mika rahoto wanda zai ƙunshi sunayen masu laifi, asarar da aka yi, da kuma shawarwarin magance matsalar gaba ɗaya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kano

এছাড়াও পড়ুন:

PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio

Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio.

Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu

“Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP.

Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa.

“Wannan cin zarafi ne da amfani da muƙami ba daidai ba, domin Akpabio na ci gaba da zama a kujerarsa duk da irin wannan zargi mai girma.

“Idan har bai da abin ɓoyewa, ya sauka don bayar da damar gudanar da bincike na gaskiya,” in ji PDP.

PDP ta nuna cewa ba wannan ne karon farko da ake zargin Akpabio da aikata irin wannan ba.

Ta ce tsohuwar Shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Dokta Joi Nunieh, ta taɓa yin irin wannan ƙorafi a kansa.

Jam’iyyar ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa da ya kare sunansa ta hanyar amincewa da bincike maimakon ƙoƙarin ɓoye gaskiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu
  • Shugabannin Larabawa Sun Amince Da Tsarin Gina Gaza Da Zai Lakume Dala Biliyan 53
  • Taro Na Uku Na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ya Yi Zama Na Biyu
  • Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda
  • Ɗan Uwan Gwamnan Kano Da Malaman NNPP Sun Koma APC
  • Jigon APC Ya Fara Yunkurin Sulhunta Kwankwaso, Ganduje Da Shekarau
  • PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio
  • Gwamna Dauda Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Zamfara Da Sakatarori 12
  • Ƙasurmugin Ɗan Ta’adda Maigemu Ya Shiga Hannu A Kebbi