Leadership News Hausa:
2025-03-10@10:44:27 GMT

Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria

Published: 10th, March 2025 GMT

Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria

Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News.

Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu

Afrika ta Kudu ta dawo daga hutun rabin lokaci cikin azama da sa rai ta kuma rage giɓin dake tsakanin ƙasashen biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kyaftin ɗin tawagar Afrika ta Kudu Success Malebana ne ta ci daga bugun fenariti.

Chidi kuma ta ƙara jefawa Nijeriya ƙwallo a ragar masu masauƙin baƙin a minti na 68, kungiyoyin biyu za su sake karawa ne a fafatawar da za a yi a filin wasa na Remo Stars, Ikenne mako mai zuwa ranar Asabar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu A Kano Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Kan Safarar Maƙudan Kuɗaɗe

Alkalin kotun ya umarci a kwace kuɗin tare da mika su ga gwamnatin tarayya, bisa tanadin dokar hana safarar kuɗaɗe ta shekarar 2022.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP
  • Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu
  • Dalilin Da Ya Sa Aka Soke Wasan Barcelona Da Osasuna
  • Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
  • Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
  • Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (2)
  • Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol
  • NNPC Da Matatar Dangote Na Gasar Rage Farashin Fetur
  • Kotu A Kano Ta Yanke Wa Wata Mata Hukunci Kan Safarar Maƙudan Kuɗaɗe