Sama da mutane 1,000 suka mutu a rikicin Siriya
Published: 10th, March 2025 GMT
Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 a cikin kwanaki biyu kacal.
Wannan tashin hankalin, ya fi shafar yankin yammacin Syria, wanda ya kara ta’azzara halin da ake ciki.
A baya dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa, an kashe akalla mutane 237 da suka hada da 142 wadanda ba mayakan ba ne a yankin gabar ruwan kasar ta Syria, tun bayan fara kazamin fada a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wadannan al’amura dai na nuni da karuwar tashe-tashen hankula, mafi muni da aka gani tun bayan faduwar gwamnatin da ta shude a watan Disambar da ya gabata.
Shugaban Syria Abu Mohammed al-Jolani ya yi kira da a samar da zaman lafiya da hadin kan kasa bayan tashe tashen hankula a kasar a baya-bayan nan, yana mai jaddada cewa abubuwan da ke faruwa na daga cikin kalubalen da ake iya fuskanta.
Wannan sabon lamari na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun HTC suka kara kaimi wajen murkushe ragowar tsoffin sojojin Syria a lardunan Latakia, Tartus da Hama.
Ana gwabza fada ne a yankin gabar tekun arewa maso yammacin kasar, inda galibin al’ummar kasar ke da ‘yan tsiraru ‘yan Alawiyya, wanda shi ma tsohon shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya fito.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fararen hula 162 sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan a lardunan gabar tekun Syria
Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar.
Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR.
Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka kama mutanen, bisa tuhumar cewa suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Bashar Assad, a kan haka suka yanke musu hukuncin kisa a nan take kuma suka kashe su.
Kungiyar ta ce wannan matakin na nuni da irin mawuyacin hali mai matukar hadari da Syria ta fada a ciki, inda ake ci gaba da cin zarafi jama’a da kuma muzguna musu da sunan daukar fansa a kan tsiraru marasa rinjaye.
Wasu daga cikin Hotunan da aka dauka sun yadu a shafukan sada zumunta, wadanda suke nuni da manyan laifukan yaki. Rahoton ya ce wasu daga cikin faifan bidiyo sun nuna lokacin da jami’an tsaron sabuwar suka harbe wasu ‘yan kasar Syria da ba su dauke da makami, wadanda aka wulakanta su kafin a yi musu kisan gilla.