Shugaban Ghana ya ziyarci kasashen Sahel da suka balle daga Ecowas
Published: 10th, March 2025 GMT
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas.
Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel.
Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsaro.
Kafin Nijar, John Dramani Mahama ya je Mali inda Janar Assimi Goïta ya tarbe shi. A cewar fadar shugaban kasar Ghana, ganawar da aka yi tsakanin mutanen biyu ta ba da damar fara tattaunawa kan karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro.
Shugaban na Ghana ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana mahimmancin kasuwanci ta hanyar hanyar tashoshin jiragen ruwa na Ghana da ke Tekun Atlantika ga Mali.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa
Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba.
Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a ranar 26 ga Maris.
A yanzu sabon kundin tsarin mulkin kasar ya jera harsuna goma sha daya da ake magana da su na Nijar, inda ya amince da Hausa a matsayin harshen kasa.
Harshen Hausa dai shi ne yaren da aka fi amfani da shi a duk fadin Nijar.
A kwanakin baya sabbin hukumomin kasar da ke da suka raba gari da kasar faransa wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka, ta fice daga kungiyar bunkasa harshen faransaci ta OIF.
Sannan kuma a baya-bayan nan kasar ta sauya sunayen wasu tituna a birnin Yamai masu dauke da sunayen Faransanci, a wani mataki na kawo karshen duk wata alama ta mulkin mallaka na turawan faransa.