Aminiya:
2025-03-10@13:21:34 GMT

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano

Published: 10th, March 2025 GMT

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai.

Mun bai wa Akpabio sa’o’i 48 ya dawo da Sanata Natasha — SERAP Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata

Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na dare, inda maharan su uku riƙe da bindigogi da adduna suka rufar wa gidan Alhaji Yusha’u.

Kazalika, maharan sun arce da wayoyin hannu da kuɗaɗe da ba a kai ga tantance ko nawa ba ne.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin da bincike ya soma gudana a kansa.

SP Kiyawa ya ce tuni ’yan sanda suka fara farautar ɓata-garin domin ceto matashin da aka yi garkuwa da shi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne ’yan sanda suka kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan ta ƙwace makamai da alburusai da kuɗi kimanin naira 1,028,800 a unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Kano mahara

এছাড়াও পড়ুন:

Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu

Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu.

A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’.

Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba

Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993.

“Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin Babangida, ƙoƙari ne na sauya tarihi da gangan.

“Shekaru da dama, wasu mutane na ƙoƙarin ɓata haƙiƙanin abin da ya faru a wannan lokaci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya,” in ji sanarwar.

Iyalan Abacha sun jaddada cewa a lokacin da aka soke zaɓen, Janar Abacha ba shi ne Shugaban Ƙasa ko Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ba.

Sun ce Babangida ne, ya ke da cikakken iko, kuma shi kaɗai ne ke da alhakin duk wani hukunci da gwamnatinsa ta yanke.

“Hukuncin soke zaɓen ya fito ne daga gwamnatin Janar Ibrahim Babangida, wanda yake a matsayin Shugaban Ƙasa, yana da cikakken iko kuma shi ne ke da alhakin duk wani abu da gwamnatinsa ta aikata,” in ji sanarwar.

Haka kuma, iyalin Abacha sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji “ƙagaggun labarai da ake ƙirƙira don karkatar da tunanin jama’a saboda wasu muradu na siyasa ko na ƙashin kai.”

Sun jaddada cewa, “Ba za mu yarda a ɓata tarihin mahaifinmu da wasu zarge-zargen banza da aka ƙirƙira don kare waɗanda suka aikata laifin ba.”

“Mun kuma ga dacewar tunatar da mutane cewa a lokacin da rayuwar Janar Babangida ta shiga hatsari, Janar Abacha ne, ya kawo masa ɗauki, ya tabbatar da cewa ba a cutar da shi ba,” in ji iyalan.

A ƙarshe, sun soki littafin ‘A Journey in Service’, inda suka ce littafin bai bayar da sahihin tarihin abubuwan da suka faru ba.

“A cewar wani da ya yi sharhi a kan littafin, gaskiya, amana ba halaye ba ne da za a alaƙanta su da marubucin ba,” in ji su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kano, Sun Sace Mutum Ɗaya
  • Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu
  • An harbe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a Kwara
  • Hadin Kai Ne Kadai Zai Kai Masana’antar Kannywood Tudun Mun Tsira -Ado Ahmed Gidan Dabino
  • Oficin Jakadan Iran A MDD Ya Ce Babu Wani Sako Da Suka Karba Daga Shugaban Kasar Amurka
  • Mun kama ’yan bindiga da suka yi kutse a Kano — ’Yan sanda
  • An Bukaci ‘Yan Su Matsa Kaimi Har Sai Anbiya su Hakokinsu
  • An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
  • An Bude Cibiyoyin Ciyar Da Masu Azumi A Dan Modi Na Garin Kafin Hausa