Leadership News Hausa:
2025-04-10@06:45:17 GMT

Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Koma SDP

Published: 10th, March 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Koma SDP

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.

Majiyoyi sun ce ficewarsa ta biyo bayan rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar. A cewar El-Rufai, APC ta kauce daga ainihin manufofinta, don haka ba zai ci gaba da kasancewa a cikinta ba.

Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

Koma wa SDP ya haifar da raɗe-raɗin cewa yana shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, lamarin da ke nuna sauyar tsarin siyasa a Nijeriya, idan har za a samu ɗan takara daga arewa a 2027.

A halin yanzu, shugabannin APC na nazarin tasirin wannan sauyi, yayin da SDP ke maraba da zuwansa a jam’iyyar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi

 

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin samar da kungiyar masu amfani da ruwan sha da makamantan su na 2025 ya zama doka.

Kudirin wanda zai bunkasa samar da ruwan sha da amfani a fadin jihar, ya samu karbuwa da amincewa cikin gaggawa saboda muhimmancin ruwa ga rayuwar al’umma.

Shugaban majalisar dokoki ta jihar, Yusuf Dahiru Liman ya sanar da amincewa da kudiring a lokacin zaman majalisar a Kaduna.

Kudirin da bangaren zartarwa na jihar ya aike da shi majalisar, an mika shi ga kwamitin ayyukan al’umma da samar da ababen more rdayuwa domin yin nazari akai, inda daga bisani ‘yan kwamitin suka tuntubi masu ruwa da tsaki a bangaren domin jin ba’asin su, sannan ya gabatar da bayanan da ya tattara da kuma shawarwari a zauren majalisar.

Shugaban kwamitin ayyukan al’umma da ababen more rayuwa, Alhaji Nasir Idris ya yi bayanin alfanun kudirin wajen bunkasa albarkatun ruwa a jihar da ma kasa baki daya.

Alhaji Nasir Idris ya lura cewa an amince da kudirin ne cikin hanzari duba da muhimmancin ruwa, wanda ya kasance wajen inganta lafiyar al’umma da zamantakewar su a jihar.

A wani labarin kuma, majalisar dokoki ta jihar Kaduna ta karba tare da amince da rahoton korafin da aka gabatar mata akan wani dan kwangila da aka baiwa aikin gina kasuwar Tudun Saibu ta Zamani a karamar hokumar Soba ta Jihar.

Da yake gabatar da rahoton binciken, Shugaban kwamitin bunkasa kasuwanni kuma dan majalisar mai wakiltar mazabar Jama’a, Mr. Ali Kalat aikin hadin gwiwa ne tsakanin majalisar karamar hukumar soba da wani kamfani Bebeji Integrated Services Limited wanda dan kwangilar ya gaza cika alkawarin da aka yi da shi,

A cewar rahoton, an kulla yarjejeniyar ce tun a watan Afrilun 2021 sannan a na sa ran kammalawa cikin kwanaki 90, sai dai dan kwangilar ya rushe gine-ginen tsohuwar kasuwar ce kawai ba tare da aza harsashin gina wata ba, duk da ikirarin da ya yi na cewa ya kai bulo 30,000 da siminti rabin tirela.

Kwamitin ya gano dan kwangilar ya saba yarjejeniya sannan ya bada shawarar a soke kwangilar domin a ba wani da ya cancanta domin gudanar da aikin.

Daga karshe kafatalin ‘yan majalisar sun amince da rahoton da kuma shawarwarin kwamitin.

Shamsuddeen Mannir Atiku

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana
  • ’Yan bindiga na neman N100m kafin sakin Faston da suka sace a Kaduna
  • Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi
  • Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi
  • Zulum: Boko Haram na sake kwace iko da wasu yankuna a Borno
  • Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum
  • Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista
  • ɗin aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kudin gwamnati — Tsohon Minista
  • Gwamnan Kano Ya Sadaukar Da Lambar Yabonsa Ga ‘Ya’yan Marasa Ƙarfi A Kano
  • Jam’iyyar Labour Ta Yi Barazanar Dakatar Da Peter Obi Da Gwamna Otti